Gabas Ta Tsakiya

Sojojin Isra’ila sun azabtar da yaro ɗan shekara ɗaya don tilasta wa mahaifinsa amsa tambayoyi

Sojojin sun azabtar da yaron a gaban mahaifinsa ta hanyar ƙona ɗaya daga cikin ƙafafunsa da sigari, tsaga masa jiki da saka ƙusoshi a kafarsa, kamar yadda gidan talabijin na Falasɗinu ya ruwaito.

Newstimehub

Newstimehub

23 Mar, 2026

378c1975fcbe1c941d45af4bdefdd3c37773317eb61caa008d5c740fd28af47a

Sojojin Isra’ila sun azabtar da wani yaro ɗan shekara ɗaya a tsakiyar Gaza domin tilasta wa mahaifinsa amsa tambayoyi a yayin da suke bincike, kamar yadda gidan talabijin na Falasɗinu ya ruwaito ɗan jaridar ƙasar Osama Al-Kahlout yana bayyanawa.

Gidan talabijin ɗin ya nuna bidiyon raunukan da aka ji wa yaron, mai suna Karim, bayan sojojin na Isra’ila sun kama shi a kusa da sansanin ‘yan gudun hijira na Al-Maghazi a tsakiyar Gaza.

Shaidu sun ce mahaifin yaron, Osama Abu Nassar, ya shiga tashin hankali bayan mutuwar dokin da yake amfani da shi wajen samun kudin shiga.

Yayin da yake tafiya da ɗansa don siyan kayayyaki, sai ya aka rutsa da shi a lokacin da ake musayar wuta a kusa da gidansa inda sojojin Isra’ila suka tilasta masa ya bar dansa mai watanni 18 a kasa sannan ya tafi zuwa wani shingen binciken soja da ke kusa, inda aka yi masa tambayoyi.

Sojojin sun azabtar da yaron a gaban mahaifinsa ta hanyar ƙona ɗaya daga cikin ƙafafunsa da sigari, tsaga masa jiki da saka ƙusoshi a kafarsa, kamar yadda rahoton likita ya tabbatar.

Rahoton ya ce yaron ya samu tabon ƙuna daga sigari da kuma ramuka a kafarsa da ƙusoshi suka haifar.

An saki yaron bayan kusan awanni 10 sannan aka miƙa shi ga iyalinsa ta hanyar Kwamitin Red Cross na Duniya a Al-Maghazi, yayin da mahaifin ke ci gaba da zama a tsare a hannun sojojin Isra’ila.

Iyalin sun roki kungiyoyin kasa da kasa da su shiga tsakani domin a sako mahaifin don ya ci gaba da karbar magani.