Ƙasar Iran ta yi kira ga ƙasashen Gabas ta Tsakiya su kafa wani sabon ƙawancen tsaro da na soji wanda zai fware ƙasashen Amurka da Isra’ila, lamarin da ke nuna yunƙurin sauya fasalin tsaron yankin a daidai lokacin da rikici ke ƙara ta’azzara.
Ebrahim Zolfaghari, kakakin babbar hedkwatar Khatam al-Anbiya kasar Iran, ya bayyana a ranar Laraba cikin wani saƙo na bidiyo cewa, lokaci ya yi da kasashen yankin za su ɗauki nauyin kare kansu tare ba tare da dogaro da wasu ƙasashen waje ba.
Ya bayyana hare-haren da Amurka da Isra’ila ke kai wa Iran a matsayin wani sauyi, inda ya bayyana su a matsayin “sabuwar kakar” da ke buƙatar haɗin kan ƙasashen Musulmai.
Kiran samar da sabon tsari a yankin
Zolfaghari ya buƙaci ƙasashen Larabawa da na Musulmai su kafa haɗin gwiwar tsaro da za a gina kan addini da alaƙar yanki guda, yana mai bayar da hujjar cewa dogaro da ƙasashen waje ya gaza samar da kwanciyar hankali.
“Dole ne mu haɗa kai don tabbatar da tsaronmu,” in ji shi, yayin da yake kira a samar da wata yarjejeniya ta bai-ɗaya bisa koyarwar Musulunci. Wannan shawara na nuna ƙoƙarin Iran na neman goyon bayan ƙasashen yankin, yayin da take fuskantar matsin lamba na soja.
Yaƙi ya sauya fasalin kawance
Wannan kira ya zo ne yayin da ake ci gaba da gwabza faɗa sakamakon hare-haren Amurka da Isra’ila kan Iran, inda Tehran ke mayar da martani ta hanyar amfani da makamai masu linzami da jiragen marasa matuƙa kan Isra’ila da ƙasashen da ke da sansanonin sojin Amurka a cikinsu.
Har yanzu ba a tabbatar ba ko ƙasashen yankin — waɗanda da dama suna da alaƙar tsaro da Amurka — za su amince da irin wannan ƙawance, amma shawarar ta nuna gagarumar ɓaraka ta fuskar siyasa da kuma bambancin muradai game da makomar Gabas ta Tsakiya.














