Rahotanni sun nuna cewa babbar cibiyar sarrafa iskar gas mai ruwa (LNG) ta duniya da ke Qatar ba za ta dawo cikakken aiki ba cikin gaggawa bayan lalacewar da ta samu sakamakon hare-hare. Kamfanin binciken makamashi na Rystad Energy ya bayyana cewa matsalar ba wai kuɗi ba ce, sai dai ƙarancin muhimman kayan aiki da ake bukata wajen gyara cibiyar.
Lalacewar da aka samu a wasu manyan sassan cibiyar a Ras Laffan ta rage ƙarfin samar da LNG da kusan kashi 17%, wanda ya kai kimanin ton miliyan 12.8 a shekara. Babbar matsalar ita ce jirage masu ƙarfi (turbines) da ake bukata domin gudanar da ayyukan sanyaya gas suna fuskantar jinkiri wajen isowa, inda ake hasashen zai ɗauki tsakanin shekaru biyu zuwa huɗu kafin a samu su.
Masana sun ce akwai kamfanoni kaɗan ne a duniya da ke kera irin waɗannan kayan aiki, kuma tuni suka cika da buƙatu daga sassa daban-daban kamar cibiyoyin bayanai (data centers) da kuma ƙoƙarin rage amfani da kwal. Wannan ya sa ko da an tanadi kuɗi nan take, jinkirin samar da kayan aiki zai iya ja da baya har zuwa shekaru biyar kafin a dawo cikakken aiki.
Wannan matsala na cikin wani babban girgiza a fannin makamashi a yankin Gabas ta Tsakiya, inda hare-hare suka lalata cibiyoyin mai da gas da dama. Ana hasashen kudin gyaran ya kai akalla dala biliyan 25, kuma hakan zai iya ƙaruwa. Rashin cikakken aiki a Qatar zai ci gaba da shafar kasuwannin duniya, musamman Turai da Asiya da ke dogaro sosai da LNG daga kasar.














