Nijeriya

Dakarun Amurka da na Nijeriya sun kashe mataimakin shugaban Daesh, Abu-Bilal al-Minuki: Trump

Nijeriya ta daɗe tana fama da hare-haren ta’addanci a sassa daban-daban na ƙasar, cikinsu har da na ƙungiyar Boko Haram da ISWAP mai alaƙa da Daesh.

Newstimehub

Newstimehub

16 May, 2026

2026 05 16t040317z 1 lynxmpem4f01v rtroptp 3 china usa

Shugaban Amurka Donald Trump ranar Jumma’a da tsakar dare ya sanar cewa dakarun ƙasar da na Nijeriya sun kashe mataimakin shugaban ƙungiyar Daesh a duniya, a wasu hare-hare ta sama na haɗin gwiwa.

“A daren yau, bisa umarnina, jajirtattun dakarun Amurka da Sojojin Nijeriya sun aiwatar da shirin da aka tsara cikin tsanaki kuma mai cike da hatsari inda suka kawar da ɗanta’adda mafi hatsari a duniya daga fagen daga,” in ji Trump a wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na sada zumunta na Truth Social.

Trump ya ce Abu-Bilal al-Minuki ya yi “tsammani zai ɓiya a Afirka,” inda ya yi iƙirarin cewa majiyoyin hukumomin leƙen asirin Amurka sun riƙa bibiyar duk wani motsinsa.

“Daga yanzu ba zai sake addabar al’ummar Afirka, ko kuma ya kitsa hare-hare kan Amurkawa,” in ji shu, inda Trump ya ƙara da cewa an yi “mummunar ɓarna” ga ayyukan Daesh a duniya sakamakon kisansa.

Ya gode wa gwamnatin Nijeriya bisa haɗin gwiwa wajen gudanar da wannan aiki.

Nijeriya ta daɗe tana fama da hare-haren ta’addanci a sassa daban-daban na ƙasar, cikinsu har da na ƙungiyar Boko Haram da ISWAP mai alaƙa da Daesh.