Gabas Ta Tsakiya

Sojojin Amurka sun kai hari kan jiragen yaƙi na ruwa da wuraren makamai masu linzami a kudancin Iran

Sojojin Amurka sun kai jerin hare-hare ta sama a kudancin Iran, kan abin da Cibiyar Bayar da Umarni ta Sojojin Amurka ta bayyana a matsayin wuraren kai hare-haren makamai masu linzami da ƙananan jiragen ruwa da ake amfani da su wajen dasa nakiyoyi.

Newstimehub

Newstimehub

26 May, 2026

b0ffca68e1bb347a13f3b84b7b315b9b4e2fd517b2e336859bae86fb98769410

Amurka ta sanar da cewa ta kai jerin hare-hare a kudancin Iran waɗanda suka nufi tashoshin harba makamai masu linzami da jiragen ruwa da ake zargin suna sanya nakiyoyi.

“Sojojin Amurka sun gudanar da hare-haren kare kai a kudancin Iran a yau don kare sojojinmu daga barazanar da rundunonin Iran ke haifarwa,” in ji kakakin Cibiyar Bayar da Umarnin Soji ta Amurka (CENTCOM), Capt. Tim Hawkins, a cikin wata sanarwa da ya aike wa Fox News.

Wuraren da aka kai harin sun haɗa da tashoshin harba makamai masu linzami da jiragen ruwa na Iran da ke ƙoƙarin dasa nakiyoyi. “Cibiyar bayar da Umarni ta Amurka na ci gaba da kare rundunarmu yayin da take taka tsantsan a lokacin tsagaita wuta da ke ci gaba da aiki,” in ji Hawkins.

Hawkins bai bayar da ƙarin bayani kan hare-haren ba, amma kafofin watsa labarai na Iran sun ruwaito tun da farkon a ranar Litinin cewa an ji ƙarar fashe-fashe a birnin Bandar Abbas a kudancin Iran da kuma a yankuna a kusa da Sirik da Jask a gabar Tekun Fasha.

Kamfanin dillancin labarai na Fars, mai alaƙa da gwamnati, ya ce mazauna Bandar Abbas sun bayar da rahoton jin fashe-fashe da dama, inda ya da ƙara da cewa ba a san takamaimen ainihin wurin da aka samu fashe-fashen ba har zuwa lokacin bayar da rahoton.

Kafar ta kuma ruwaito cewa an ji irin waɗannan ƙara a lokaci guda a yankunan da ke daura da Sirik da Jask a kudancin Iran da ke kallon gabar Tekun Fasha.

Wata kafar labarai ta Mehr, wadda ita ma kusan na gwamnati ce, ta ruwaito cewa lamura sun daidaita a birnin tashar Bandar Abbas bayan hare-haren.