Nijeriya

Janar ɗin Nijeriya mai ritaya da matarsa sun roƙi gwamnati ta ceto rayuwarsu daga masu garkuwa

A cikin bidiyon, matar tsohon janar ɗin ta bayyana cewa masu garkuwar na neman a saki mambobinsu uku waɗanda suka haɗa da Sani, Aminu, da Nasiru. Haka kuma suna neman a mayar musu da dabbobin da ake zargin an ƙwace daga hannunsu.

Newstimehub

Newstimehub

6 Jun, 2026

9c1335330387629398437c2ed950921a9f69a27bc28c4c1558e5f69a29bab79e

Wani tsohon jami’in sojojin Nijeriya mai ritaya, Manjo Janar Abubakar Rabe, tare da matarsa, waɗanda aka yi garkuwa da su mako guda da ya wuce a kan hanyar Karaduwa–Matazu a Jihar Katsina, sun roƙi gwamnati da ta gaggauta yin duk abin da ya dace domin ceto rayuwarsu.

Masu garkuwar sun fitar da wani bidiyo da ke nuna ma’auratan a cikin daji a tsare. A cikin bidiyon mai tsawon mintuna huɗu da daƙiƙa biyu da ke yawo a kafafen sada zumunta, an gansu a tsaye suna karanta buƙatun da masu garkuwar suka umurce su.

A cikin bidiyon, matar tsohon janar ɗin ta bayyana cewa masu garkuwar na neman a saki mambobinsu uku waɗanda suka haɗa da Sani, Aminu, da Nasiru. Haka kuma suna neman a mayar musu da dabbobin da ake zargin an ƙwace daga hannunsu.

Ta bayyana cewa an kama biyu daga cikin waɗanda ake tsare da su a Jikamshi, yayin da aka kama na uku a Kano.

Ta ƙara da roƙon gwamnatin Jihar Katsina da shugabannin ƙananan hukumomi biyar da su shiga tsakani domin a biya waɗannan buƙatu domin samun ’yancinsu.

Shi ma tsohon janar ɗin ya yi gajeriyar magana a cikin bidiyon, inda ya yi kira da a kwantar da hankali tare da neman a yi ƙoƙarin samar da zaman lafiya, yana mai cewa masu garkuwar sun nuna sha’awar tattaunawa da zaman lafiya.

Ba a ambaci neman kuɗin fansa a cikin bidiyon ba.

Rahotanni sun ce Manjo Janar ɗin mai ritaya yana kan hanyar tafiya zuwa Katsina a ranar Asabar tare da matarsa, Hajiya Amina Abubakar, da direbansu, Abdullahi Sa’idu, lokacin da aka tare motocinsu a kan hanyar Marabar Musawa–Kafinsoli a ƙaramar hukumar Matazu.