Babbar Kotun Jihar Sokoto ta yanke wa mutum uku hukuncin kisa ta hanyar rataya bayan samunsu da laifukan da suka shafi ta’addanci da yaɗa makamai ba bisa ka’ida ba.
Waɗanda aka yanke wa hukuncin sun haɗa da Yusuf Muhammad (wanda aka fi sani da Sallau), ɗan ƙasar Nijar; Jabbi Alhaji Yalle; da Kabiru Muhammad.
Hukumar Tsaro ta Farin Kaya (DSS) ta kama su ne a ranar 13 ga Yunin 2025 ta hannun sashenta na yaƙi da ta’addanci, bisa zarginsu da hannu a ayyukan safarar makamai da ta’addanci da suka shafi ƙetare iyakoki.
An saurari shari’ar mai lamba SS/45c/2026 a gaban Mai Shari’a Muhammad Nuraddeen Bello na Kotun Jihar Sokoto mai lamba 23.
Yayin da yake yanke hukunci, Mai Shari’a Bello ya samu mutanen ukun da laifukan da ake tuhumarsu da su, tare da yanke musu hukuncin kisa ta hanyar rataya.
Kotun ta kuma bayar da umarnin kwace duk kuɗaɗen da aka samu a hannunsu tare da miƙa su ga Gwamnatin Tarayya.
Mai Shari’a Bello ya ce: “Wannan hukunci shi ne sabuwar nasara a jerin shari’o’in da DSS ta samu nasarar gurfanarwa, a ci gaba da ayyukanta na yaƙi da ta’addanci da ƙungiyoyin aikata manyan laifuka da ke aiki ta hanyar ƙetare iyakokin Nijeriya.”
Wannan hukunci ya zo ne kusan makonni biyu bayan da Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta yanke wa wasu mutum biyar da DSS ta kama a ranar 31 ga Mayun 2026 hukuncin ɗaurin shekaru 25 a gidan yari kowannensu.
An kama mutanen ne saboda zarginsu da hannu a harin da aka kai makarantar St. Mary’s Catholic School da ke Papiri a Jihar Neja a ranar 21 ga Nuwamban 2025.
Mai Shari’a Binta Nyako ce ta yanke musu hukuncin bayan sun amsa laifuffuka huɗu da suka shafi ta’addanci, ciki har da wasu ‘yan ƙasar Nijar biyu da ke cikin waɗanda ake tuhuma.
Laifukan sun haɗa da bayar da goyon baya wajen aikata ayyukan ta’addanci, wanda ya saɓa wa Sashe na 16 na Dokar Hana da Yaƙi da Ta’addanci ta shekarar 2022, da kuma Dokar Makamai.
A tuhuma ta farko, an zargi mutanen da haɗa baki domin taimaka wa wani ɗan ta’adda ta hanyar amincewa da taka rawa wajen safarar bindigogi kirar AK-103 guda 15 da harsasai masu rai kimanin 1,434 na girman 7.62mm, daga yankin Diffa na Jamhuriyar Nijar zuwa ga wani Malam Ahmad, wanda ake zargin mamba ne na ƙungiyar Boko Haram da ke yankin Borgu na Jihar Neja.
An bayyana cewa hakan laifi ne da ya saɓa wa Sashe na 26(1) na Dokar Hana da Yaƙi da Ta’addanci ta shekarar 2022.
Hukumar DSS ta kama waɗannan mutanen ne a wurare daban-daban.

















