Nijeriya

An kama mutane 10 da ake zargi da kashe shugaban ƙungiyar Fulani ta MACBAN na jihar Benue a Nijeriya

An kama wadanda ake zargin ne a daren 27 ga Yuni a yayin wani aiki samame da tawagar sashen dabaru na rundunar ta gudanar a karamar hukumar Otukpo, in ji mai magana da yawun yansanda jihar Benue.

Newstimehub

Newstimehub

29 Jun, 2026

660a2ae1fafe2d8f549623b10974520555aa5d519f7c3b552e479f6ed0dc6283

Rundunar ‘yansandan na Nijeriya ta ce ta kama mutane 10 da ake zargi da hannu a kisan Shugaban ƙungiyar makiyaya ta Miyetti Allah Cattle Breeders Association of Nigeria (MACBAN) reshen jihar Benue, Ardo Risku Mohammed da wani Yakubu Isa.

Jami’ar Hulɗa da Jama’a ta rundunar, DSP Udeme Edet, ce ta bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ta fitar ranar Lahadi a birnin Makurdi.

Edet ta ce kamen ya biyo bayan bayanan sirri da ta tattara da inda ta yi amfani da su wajen gudanar da aikinta.

Ta ce an kama waɗanda ake zargin ne ranar 27 ga Yuni da daddare a yayin wani samame da sashen dabaru na rundunar ya gudanar a Ƙaramar Hukumar Otukpo.

Mutanen da ake zargin su haɗa da Titus Thyodenda, mai shekaru 25; da Sam Utibe, mai shekaru 20; da Owoicho Ameh, mai shekaru 18; da Sunday Useni, mai shekaru 21; da Sunday Ogbanje, mai shekaru 46; da Daniel Raphael, mai shekaru 23; da John Adokole, mai shekaru 24; da Samuel Ogazi, mai shekaru 32; da Daniel Agbo Daniel, mai shekaru 25; da kuma James Onazi, mai shekaru 30, kamar yadda sanarwar mai magana da yawun rundunar ‘yansanda ta bayyana.

Kazalika Edet ta ce Kwamishinan ‘yansandan jihar, Cletus Nwadiogbu, ya jinjina wa tawagar sashen dabaru rundunar da masu bincike bisa saurin ɗaukar mataki da kuma nuna ƙwarewa wajen kama mutanen da ake zargi.

Haka kuma, ta ce Kwamishinan ya ba da tabbacinsa ga mazauna yankin wajen ci gaba da bincike don gano da kuma kama sauran mutanen da ke da hannu a wannan mummunan aiki.

“Rundunar za ta ci gaba da jajircewa wajen tabbatar da cewa an gurfanar da duk waɗanda aka samu da laifi a gaban kotu don fuskantar hukunci.

“Muna kira ga mazauna yankin da su kwantar da hankalinsu, su ci gaba da ba da haɗin kai ga hukumomin tsaro da kuma samar da bayanai masu amfani waɗanda za su iya taimakawa wajen ci gaba da bincike,” a cewar sanarwar.