Turkiyya, da Saudiyya da Pakistan sun rattaba hannu kan wata muhimmiyar yarjejeniyar tsaro ta haɗin gwiwa a birnin Makka, wadda ta tanadi cewa za a ɗauki harin makami kan ɗaya daga cikin ƙasashen ukun a matsayin hari a kan dukkaninsu.
Yarjejeniya, wadda Shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdogan, da Yariman Mai Jiran Gado na Masarautar Saudiyya Mohammed bin Salman da Firaministan Pakistan Shehbaz Sharif suka sanya wa hannu a ranar 7 ga Agusta; na nufin ƙarfafa kariyar kai da haɗakar tsaro ta haɗin gwiwa tsakanin ƙasashen ukun.
An bayyana yarjejeniyar a matsayin shaida ta zurfin alaƙar tarihi, da ‘yan’uwantaka mai ɗorewa, da ƙawancen Musulunci da kuma muradun dabarun da suka haɗa su, sannan an fito da ita fili a Turkiyya ta hanyar wani kamfen na musamman na isar da sako da ido zai iya gani.
Allunan nune-nune na zamani, da haskaka gine-gine da manyan saƙonni sun sauya wasu fitattun wurare a Ankara da Istanbul zuwa dandamalai na nuna saƙonnin yarjejeniyar Makka ta haɗin kai, haɗin gwiwa da makoma ɗaya.
Ga wasu daga cikin muhimman wuraren da aka haskaka a matsayin wani ɓangare na kamfen ɗin:
Ginin Ofishin Sadarwa na Fadar Shugaban Kasa — Ankara
Ginin Ofishin Sadarwa na Fadar Shugaban Ƙasa a Ankara ya kasance ɗaya daga cikin fitattun wurare a babban birnin da aka zaɓa don kamfen ɗin.
Bidiyon zamani da aka ringa nunawa ya haskaka yarjejeniyar Makka da saƙonta na haɗin gwiwa mai muhimmanci da ƙawance tsakanin Turkiyya, Saudiyya da Pakistan.
Ginin Turk Telekom — Ankara
An kuma nuna saƙon a ginin Turk Telekom a Ankara.
An gabatar da irin waɗannan nunin a reshen Turk Telekom fiye da 600 a faɗin Turkiyya, wanda ya faɗaɗa kamfen ɗin daga babban birni zuwa ko’ina cikin ƙasar.
Atakule — Ankara
Daya daga cikin wuraren da suka fi shahara a Ankara, Atakule, shi ma an haskaka shi a matsayin wani ɓangare na kamfen ɗin.
Abubuwan da aka nuna sun jaddada jigogin yarjejeniyar ta haɗin gwiwa, haɗin kai da makoma ɗaya.
Cibiyar Al’adu ta Ataturk — Istanbul
A Istanbul, Cibiyar Al’adu ta Ataturk ta zama wani fage mai haske don kamfen ɗin.
Nune-nune a gani sun gabatar da yarjejeniyar Makka a matsayin alamar haɗin kai da ƙawancen ƙasashe ukun.
Gadar Shahidai ta 15 ga Yuli — Istanbul
Kamfen ɗin ya kai ga ɗaya daga cikin muhimman wurare a Istanbul, Gadar Shahidai ta 15 ga Yuli, wadda ke haɗa sassan Turai da Asiya na birnin.
Nunin ya isar da saƙon yarjejeniyar ta kan ɗaya daga cikin manyan alamu na biranen Turkiyya.
Hasumiyar Galata — Istanbul
Hasumiyar Galata mai tarihi ma an haskaka ta a matsayin wani ɓangare na kamfen ɗin.
Nunin ya kawo saƙon yarjejeniyar Makka zuwa ɗaya daga cikin fitattun wurare a Istanbul, yana sadar da haɗin gwiwar tsaro ta zamani da rawar da birnin ya taka tsawon ƙarnoni a matsayin wata mahaɗa tsakanin yankuna.

















