Shugaban Amurka Donald Trump ya ce an kwance ko kuma an cire dukkan abubuwan fashewa daga tekun ƙasa da ƙasa a Mashigar Hormuz kuma an shaida wa Iran cewa duk wani jirgi ko jirgin ruwa da aka gani yana dasa bam za a lalata shi.
A cikin wani rubutu da ya fitar a shafin Truth Social ranar Talata, Trump ya ce Amurka, ta hanyar rundunar sojin sararin samaniyarta, tana kallon “kowane murabba’i” na mashigar, wadda muhimmiyar hanyar ruwa ce wajen jigilar kayayyaki a duniya.
“Akwai manufar ba-sani-ba-sabo kan dasa abubuwan fashewa da ke aiki nan-take kuma da dukkan karfi,” in ji Trump.
Amurka da Iran ba su kai hare-haren sama kan sojojin junansu ba tsawon makonni, amma hare-haren da ake kai wa jiragen ruwa a mashigar Hormuz sun ci gaba yayin da ɓangarorin biyu ke fafatawa kan iko da mashigar tekun ‘yar ƙarama.
Bayanan wucin gadi daga kamfanin bin diddigin jiragen ruwa na Vortexa sun nuna cewa man fetur da ya ratsa mashigar ruwan ya kai ganga miliyan biyar a ranar Litinin, ƙasa da ganga miliyan 20 a kowace rana kafin yaƙin ko kuma kusan ɗaya daga cikin ganga biyar da ake amfani da shi a duk duniya.
Iran da Oman sun tattauna kan mafita
A halin yanzu, ministocin harkokin waje na Iran da Oman sun ce sun tattauna kan tsarin hanyar wucin gadi a Mashigar Hormuz da kuma aikin kwance abubuwan fashewa a hanyar ruwan, wanda dukkansu ke maƙwabtaka da ita.
Ƙasashen biyu sun nemi daidaita hanyoyin sufuri ta hanyar Mashigar Hormuz, kamar yadda aka rubuta a cikin yarjejeniyar fahimtar juna tsakanin Amurka da Iran, bayan da hanyar ruwan ta zama batun tashin hankali a yakin Gabas ta Tsakiya.
Ministan Harkokin Waje na Oman Badr al-Busaidi da Ministan Harkokin Waje na Iran Abbas Araghchi “sun tattauna kan tsarin da zai iya samar da tushe mai amfani da kuma aiwatarwa don ci gaba” a tattaunawar da aka yi a Tehran, in ji wata sanarwa ta haɗin gwiwa da Oman ta watsa.
Tsarin “ya haɗa da kafa hanyar haɗin gwiwa a mashigar Hormuz da kuma yarjejeniyar aiwatar da aikin haɗin gwiwa don tsaftace wajen daga abubuwan fashewa a Mashigar,” in ji sanarwar.
Tattaunawar mai ma’ana za ta ci gaba da neman “tashar jiragen ruwa ta din-din-din da kuma gudanar da ita a nan gaba a Mashigar, da kuma hanyar yaɗa bayanai, da kula da zirga-zirgar ababen hawa, da kuma samar da ayyukan zirga-zirga da tsaro da suka dace”.
Ta ƙara da cewa, tsarin “ya haɗa da samar da hanyar jiragen ruwa ta wucin gadi a Mashigar Hormuz.” Ɓangarorin biyu sun ce yana da muhimmanci a yi tattaunawa ta haɗin gwiwa da ƙasashen da ke maƙwabtaka da Tekun Fasha.

















