Kungiyar Hezbollah ta Lebanon ta sanar a ranar Talata cewa ta kai hare-hare kan sansanonin sojin Isra’ila guda uku da ke arewacin Isra’ila da kuma yankin Golan da Isra’ila ke rike da shi.
A cikin sanarwa daban-daban, kungiyar ta ce ta yi amfani da rokoki da jiragen drone masu kai harin kai-tsaye, tana mai cewa matakin martani ne ga hare-haren da Isra’ila ke kai wa Lebanon.
Hezbollah ta jaddada cewa hare-haren sun takaita ne ga wuraren soji kawai. Ta ce ta aike da jerin jiragen drone masu kunshe da bama-bamai kan tashoshin radar da dakunan sarrafa ayyuka a sansanin jiragen sama na Ramat David. Haka kuma ta kai hari kan sansanin Meron, inda aka ce an lalata wani radar da kuma ginin umarni.
A wani farmaki na daban, kungiyar ta ce ta harba rokoki masu yawa kan sansanin Nafah, hedikwatar rundunar Bashan ta 210 a yankin Golan. Wannan na zuwa ne bayan sojojin Isra’ila sun ce an ji karar kararrawar gargadi a arewacin kasar sakamakon harbo makamai daga Lebanon.
A gefe guda, Isra’ila ta ce tana kai hare-hare ne kan Hezbollah, inda ta kaddamar da farmakin sama a sassa daban-daban na Lebanon, har ma aka ji fashewa a Beirut. A ranar Litinin ma, sojojin Isra’ila sun sake kai wasu hare-haren sama a wurare da dama na kasar.














