Shugaban Nijeriya Bola Tinubu zai bar birnin Abuja zuwa Turai don fara hutun makonni uku a wani ɓangare na hutunsa na shekara-shekara.
Wata sanarwa da mai bai wa shugaban shawara kan watsa labarai da dabaru, Bayo Onanuga, ya fitar ranar Lahadi ta ce shugaban na Nijeriya zai ziyarci Landan a tafiyarsa a Turai ɗin.
“Ana tsammanin Shugaba Tinubu ya dawo gida bayan hutun aikin domin shiga fafatukar yaƙin neman zabe na zaben watan Janairun shekarar 2027,” in ji sanarwar Onanuga.

















