Nijeriya

Nijeriya ta musanta zargin goyon bayan yunƙurin ‘juyin mulki’ a Nijar

Gwamnatin Tarayyar Nijeriya ta bayyana zarge-zargen a matsayin ƙarya da yaudara, tana mai cewa an ƙirƙire su ne domin bata sunan Nijeriya da kuma haddasa rarrabuwar kawuna.

Newstimehub

Newstimehub

4 Sep, 2026

1f6566b7 4e2f 4996 b754 cae07ca07009 1788501118461

Gwamnatin Tarayyar Nijeriya ta musanta rahotannin da ke yawo cewa, ƙasar da Ƙungiyar Raya Tattalin Arzikin Kasashen Yammacin Afirka (ECOWAS) sun goyi bayan yunƙurin ‘juyin mulkin’ da bai yi nasara ba a Jamhuriyar Nijar.

Gwamnatin ta bayyana zarge-zargen a matsayin ƙarya da yaudara, tana mai cewa an ƙirƙire su ne domin ɓata sunan Nijeriya da kuma haddasa rarrabuwar kawuna.

Ƙaramin Ministan Ma’aikatar Harkokin Wajen Nijeriya, Ambasada Sola Enikanolaiye ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ma’aikatar ta wallafa a shafinta na X, inda ya ce Nijeriya ba ta taɓa goyon bayan juyin mulkin soja ba, kuma ba za ta goyi bayan duk wani yunƙurin sauyin gwamnati da ya saba wa kundin tsarin mulki a kowace ƙasa ba.

Enikanolaiye ya ce Nijeriya na ci gaba da kasancewa mai kare tsarin mulki da dimokuraɗiyya da kuma zaman lafiyar yankin.

Ya ce kasar ba za ta amince da duk wani mataki da ya saba wa doka ba, ko da wanene ya aikata shi ko kuma a wace kasa aka aikata shi.

Ministan ya kuma yi waiwaye kan sanarwar da Ma’aikatar Harkokin Wajen Nijeriya ta fitar a ranar 30 ga watan Agusta kan halin da ake ciki a Nijar.

‘‘Nijeriya ta nuna damuwa kan abubuwan da ke faruwa a makwabciyar kasar tare da yin kira da a samu hanyar lumana, mai haɗa kowa da kowa da kuma shigar da jama’a wajen dawo da zaman lafiya da tsarin mulki,’’ in ji sanarwar.

Kazalika sanarwar ta ce, ‘‘matsayin Nijeriya kan sauye-sauyen gwamnati da suka saba wa kundin tsarin mulki a bayyane yake, sannan amfani da karfi wajen warware bambance-bambancen siyasa ya saɓa wa manufofin harkokin wajen Nijeriya.’’

Karamin Ministan ya ce “Duk da cewa Nijeriya ƙasa ce mai alfahari da kasancewa mamba mai jajircewa a ECOWAS, ba daidai ba ne, kuma ƙarya ce, a ce ƙasar ta amince ko ta goyi bayan juyin mulkin soja.”

Ministan ya kuma yi kira ga ‘yan Nijeriya da ke cikin gida da waje da su yi watsi da bidiyoyi da rahotannin da ke yawo a kafafen sada zumunta, wadanda ya ce ana amfani da su wajen haifar da rarrabuwar kawuna da yaudarar jama’a.

Enikanolaiye ya sake jaddada kudurin Nijeriya na mutunta yarjejeniyar ECOWAS kan Dimokuraɗiyya da Shugabanci na gari, da kuma manufar Tarayyar Afirka ta rashin amincewa da sauyin gwamnati ta hanyar da ta saba wa kundin tsarin mulki.

Ya ce Nijeriya za ta ci gaba da aiki tare da ECOWAS, Tarayyar Afirka da sauran kasashen duniya wajen kare dimokuraɗiyya, tabbatar da bin doka da inganta zaman lafiya da kwanciyar hankali a Yammacin Afirka da yankin Sahel.

Ƙasar Nijar ta kasance cikin manyan batutuwan diflomasiyya da tsaro a yankin tun bayan juyin mulkin da sojoji suka yi a watan Yulin 2023, wanda ya hambarar da Shugaba Mohamed Bazoum.

NJuyin mulkin ya haifar da babbar matsalar siyasa da diflomasiyya tsakanin Nijar da ECOWAS, wadda ta bukaci a dawo da tsarin mulkin dimokuraɗiyya tare da kakaba wa ƙasar takunkumi.

Nijeriya, wadda ke daga cikin manyan kasashe mambobin ECOWAS, ta taka muhimmiyar rawa wajen ƙoƙarin warware rikicin.

Tun daga lokacin, dangantaka tsakanin Nijar da wasu daga cikin makwabtan ta na Yammacin Afirka ta yi tsami, yayin da rarrabuwar kawuna a siyasar yankin ta ƙara tsananta.