Rundunar ‘yansandan Nijeriya reshen Jihar Zamfara ta ce ta fara bincike domin gano wasu malaman Addinin Musulunci shida da aka sace a kan hanyarsu ta zuwa Talata Mafara a Zamfara.
Rahotanni dai sun ce malaman suna hanyarsu ta komawa gida bayan zuwa wani taron addu’a na Jam’iyyar APC a Zamfara.
‘Yansandan sun ce tuni suka baza jami’ansu domin ceto malaman da aka sace.
’Yan bindiga sun sace limaman Musulunci shida a kan hanyar Dakko–Damri da ke ƙaramar hukumar Bakura ta Jihar Zamfara.
Rundunar ’Yan Sandan Jihar Zamfara ta ce lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 11:30 na safe ranar Asabar, 12 ga Satumba, 2026, lokacin da wasu ’yan bindiga ɗauke da muggan makamai, waɗanda ake zargin suna da nagartattun makamai, suka yi wa wata mota da ke ɗauke da waɗanda lamarin ya rutsa da su kwanton ɓauna.
A cewar ’yan sandan, mutanen shida, waɗanda dukkaninsu limaman Musulunci ne, suna tafiya ne zuwa Talata Mafara lokacin da maharan suka tare su tare da yin garkuwa da su.
Rahotanni dai sun ce malaman suna hanyarsu ta komawa gida bayan zuwa wani taron addu’a na Jam’iyyar APC a Zamfara.
Bayan samun rahoton lamarin, Jami’in ’Yansanda na Sashen Bakura ya tattara jami’an rundunar, ciki har da jami’an Sashen Yaki da Manyan Laifuka na VCRU, tare da haɗin gwiwar sauran hukumomin tsaro, domin fara aikin ceto.
Jami’an tsaron sun fara wani gagarumin aikin bincike, inda suke ratsa dazuzzukan da ke kewayen yankin domin gano tare da ceto limaman da aka sace, da kuma cafke waɗanda suka aikata laifin.
Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Zamfara, CP A. M. Bello, ya umarci jami’an da ke gudanar da aikin ceton da su ƙara kaimi tare da amfani da dukkanin kayayyakin da suke da su domin tabbatar da an ceto waɗanda aka yi garkuwa da su cikin aminci.

















