Turkiyya

Zauren kotu ya dace da masu aikata laifukan yaƙi ba zauren Majalisar Ɗinkin Duniya ba: Erdogan

Shugaban Turkiyya Erdogan ya bayyana Masu aikata laifukan yaƙi bai kamata su kasance a zauren Majalisar Ɗinkin Duniya ba, sai dai a zauren kotunan da za su amsa tambayoyi kan laifukan da suka aikata da kuma jinin da suka zubar.

Newstimehub

Newstimehub

27 Sep, 2026

4db774d5 9c38 4944 96f4 c6e6f48207cb 1790427795050 main

Shugaban Recep Tayyip Erdogan, ya ce masu aikata laifukan yaƙi ya kamata su kasance a zauren kotuna maimakon a zauren Majalisar Ɗinkin Duniya, yana mai jaddada cewa dole ne a hukunta waɗanda ke aikata kisan kiyashi.

“Masu aikata laifukan yaƙi bai kamata su kasance a zauren Majalisar Ɗinkin Duniya ba, sai dai a zauren kotunan da za su amsa tambayoyi kan laifukan da suka aikata da kuma jinin da suka zubar,” kamar yadda Erdogan ya bayyana a wajen shirin rufe Kasuwar Baje-Koli ta MUSIAD karo na 21 da kuma Taron Kasuwanci na Ƙasa da Ƙasa da aka gudanar a Istanbul a ranar Asabar.

“Idan ba a hukunta waɗanda ke aikata kisan kiyashi bisa adalci da tarihi ba, irin waɗannan ta’asar za ta sake faruwa,” kamar yadda ya yi gargaɗi.

Erdogan ya sake jaddada goyon bayan Turkiyya ga Falasɗinawa, yana cewa: “Al’ummar Falasɗinawa ba su kaɗai ba ne, kuma ba a yi watsi da su ba.”

“’Yan’uwanmu maza da mata da ke Gaza ba su kaɗai ba ne a ƙoƙarinsu na neman haƙƙoƙinsu da adalci,” kamar yadda ya jaddada.

“Za mu ci gaba, gwargwadon iyawarmu, da faɗin gaskiya da kuma zama muryar waɗanda ake zalunta,” ya ƙara da cewa.

Erdogan ya yaba wa waɗanda suka fice daga zauren Majalisar Ɗinkin Duniya lokacin da Firaministan Isra’ila, Benjamin Netanyahu, ya fara jawabi.

“Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya ya mayar da martani ga masu aikata kisan kiyashi ta hanyar ficewa daga zauren,” ya ce.

Erdogan ya ƙara da cewa yankin na fuskantar “guguwar rikice-rikice mai tsanani”, yayin da tsarin duniya ke fuskantar tangarda dangane da “halaccinsa, wakilci da adalci”.

Da yake magana kan tattalin arziƙi, ya ce Turkiyya ta samu ci gaban tattalin arziƙi ba tare da katsewa ba a cikin shekaru shida suka gabata, kuma a halin yanzu ita ce ƙasa ta 16 mafi girman tattalin arziƙi a duniya, sannan ta shida mafi girma a Turai.

Ya ƙara da cewa adadin kamfanonin Turkiyya masu fitar da kayayyaki zuwa ƙasashen waje ya ƙaru daga 33,000 a shekarar 2002 zuwa 168,000 a shekarar 2025.