Gabas Ta Tsakiya

Sojin ruwan Amurka takwas sun jikkata a harin makami mai linzami da Iran ta harba a Mashigar Hormuz

Jami’an Amurka sun ce Sojojin ruwan sun shaƙi hayaƙi da kuma buguwa a kai inda suka soma samun alamu na zubar jini a kwakwalwarsu bayan harin na ranar 14 ga Satumba.

Newstimehub

Newstimehub

28 Sep, 2026

57770d57 0dd9 4af2 8e18 b47880a82543 1790574563380

Wasu sojojin ruwan Amurka takwas sun jikkata bayan harin makami mai linzami na Iran kan wani jirgin ruwa a Mashigar Hormuz, a cewar rahoton kafar NBC News, tana mai ambato jami’an Amurka uku.

Jami’an ruwan ba su samu mummunar rauni ba amma sun shaƙi hayaƙi da kuma buguwa a kai, yanayin da ya jawo tsananin ciwon kai wanda ake ganin ya taba lafiyar kwakwalwarsu.

Rundunar ta kunshi kananan jami’ai bakwai da kuma wani babba guda daya, dukkansu suna aiki a matsayin wani bangare na tawagar saukar bataliyar sojoji lokacin da harin ya auku a ranar 14 ga Satumba.

Dukka jami’an takwas sun koma bakin aiki jim kadan bayan harin, kamar yadda jami’ai suka tabbatar.

Jami’an sun bayyana cewa jirgin ruwan da aka kaiwa hari ba jirgin ruwan yakin Amurka bane da aka tura, sai dai ba su bayyana asalinsa ba.

Rahoton Mutuwar Jami’an Tsaron Amurka

Lamarin ya zo ne a daidai lokacin da ake ci gaba da bincike kan adadin asarar rayuka na Ma’aikatar Tsaro tun bayan barkewar yakin Amurka da Isra’ila da Iran a watan Fabrairu, inda jimillar adadin wadanda suka jikkata da wadanda suka mutu ke ci gaba da sauyawa a rohotanni da ake tattarawa.

Ya zuwa ranar Laraba, Tsarin Nazarin Mutuwar Jami’an Tsaron Amurka (DCAS) ya tattaro sunayen sojojin Amurka 861 da suka jikkata sakamakon yakin.

An sanya sunan dakarun sojin Amurka takwas a cikin rijistar bayanan wadanda suka mutu bayan kwanaki 10 da harin na ranar 14 ga Satumba.

Wani jami’in tsaron Amurka ya danganta jinkirin da aka samu wajen tantance alkaluman wadanda suka mutu ko suka jikkata saboda wasu alamomin rauni ba sa bayyana sai bayan wasu kwanaki. da kuma rashin iya samun rahoto a ainihin lokaci daga tsarin bin diddigin wadanda suka mutu ko suka jikkata.