Rundunar sojin Nijeriya ta kaddamar da sabbin motocin yaki masu sulke da wasu bataliyar soji uku a jihar Kebbi, a wani mataki na ƙara ƙarfafa ayyukan tsaro a yankin Arewa maso Yammacin ƙasar.
Babban Hafsan Sojin Nijeriya, Laftanar Janar Waidi Shaidu ne ya kaddamar da rundunar 28 Armoured Brigade da Garrison a Birnin Kebbi, da motocin yaki masu sulke 281 a Yauri da kuma sashen makamai na 381 a Kaoje.
Babban Hafsan Sojin ya samu wakilcin Manjo Janar Bemgba Paul Koughna, Kwamandan Runduna ta 8 ta Sojin Nijeriya kuma Kwamandan Sashe na Biyu na Rundunar Hadin Gwiwa ta Arewa maso Yamma (Operation FANSAN YAMMA).
Koughna ya ce sabbin rundunonin za su faɗaɗa ayyukan sojoji da ƙarfafa tsarin da sai ido da kuma rage lokutan da ake ɗauka wajen mayar da martani ga barazanar tsaro a yankin.
Ya umarci Mukaddashin Kwamandan Rundunar 28 Brigade, Kanal Abdullahi Umar, da ya tabbatar da cewa rundunar ta samar da isasshen ƙarfin tallafin makamai ga ayyukan sojin da ake gudanarwa.
Kazalika Kwamandan ya ce sabbin rundunonin za su ƙara ƙarfafa matakan da ake ɗauka domin dakile ayyukan ƙungiyoyin masu ɗauke da makamai da sauran barazanar tsaro a jihar Kebbi.
A cikin wata sanarwa da aka raba wa manema labarai a ranar Litinin a Birnin Kebbi, Kwamishinan Yaɗa Labarai da Al’adu na jihar Kebbi, Yakubu Ahmed, ya ce wannan ci gaba ne da ke nuna jajircewar Sojojin Nijeriya wajen magance matsalolin tsaro da ke fuskantar Jihar Kebbi musamman da kuma ƙasar baki ɗaya.
Kwamishan ya kuma yaba da gudunmawar da sauran hukumomin tsaro suka bayar, ciki har da Rundunar ‘Yan Sandan Nijeriya, Ma’aikatar Ayyukan Jiha, Rundunar Tsaro da Tsaron Farar Hula ta Nijeriya, mafarauta da sauran ƙungiyoyin ‘yan banga na al’umma, a ƙoƙarin haɗin gwiwa na kare rayuka da dukiyoyi a faɗin Jihar.
Ya yi kira da a ƙara haɗin gwiwa tsakanin sojoji da sauran hukumomin tsaro da sarakunan gargajiya da kuma al’ummomin yankin, yana mai cewa samar da zaman lafiya mai ɗorewa na buƙatar haɗin gwiwar kowa.

















