Nijeriya

Nijeriya ta ce babu tsagaita wuta da ‘yanta’addan Boko Haram da Daesh

Mai magana da yawun sojin ƙasar Manjo Janar Samaila Uba ya ce nasarorin ‘yan kwanakin nan sun nuna cewa dakarun tsaro suna ci gaba da ƙara matsi kan ƙungiyoyin ‘yan bindiga.

Newstimehub

Newstimehub

6 Nov, 2026

1b4a65ec 82bd 400f 940b 96c7b6d9bf9c 1793904172716

Sojojin Nijeriya sun bayyana a ranar Alhamis cewa babu wata yarjejeniyar tsagaita wuta da ’yan ta’addan Boko Haram da Daesh, suna mai cewa za su ci gaba da matsa musu lamba ta hanyar kai hare-hare.

Sojojin ƙasar sun shafe kusan shekaru 20 suna yaƙi da ’yan ta’adda a arewa maso gabashin Nijeriya.

Da yake magana a wani taron manema labarai kan bayanan sirri a babban birnin ƙasar, Abuja, mai magana da yawun rundunar sojin Nijeriya, Manjo-Janar Samaila Uba, ya ce nasarorin da aka samu a baya-bayan nan, ciki har da kashe ’yanta’adda, kama waɗanda ake zargi da aikata laifuka da kuma kuɓutar da mutanen da aka yi garkuwa da su, na nuna cewa dakarun tsaro na ci gaba da matsa wa ƙungiyoyin ’yanbindigar lamba.

“Ina son in bayyana ƙarara cewa babu wani abu kamar tsagaita wuta… Idan aka yi la’akari da ci gaban da aka samu a faɗin wuraren da muke gudanar da ayyuka, a bayyane yake cewa ba ma sassautawa,” in ji Uba.

Ya kuma ce Nijeriya na gudanar da tattaunawa kan haɗin gwiwar tsaro da diflomasiyya da ƙasashen yankin Sahel maƙwabta waɗanda suka fice daga Ƙungiyar Raya Tattalin Arziƙin Ƙasashen Yammacin Afirka (ECOWAS).