Jam’iyyar APC mai mulki a Nijeriya ta bayyana alhininta kan wani hatsarin mota da ya afku a Jihar Zamfara, wanda rahotanni suka ce ya yi sanadin mutuwar mambobi da magoya bayan jam’iyyar 15, yayin da mutane da dama suka jikkata.
A cikin wata sanarwa da Sakataren Yaɗa Labaran Jam’iyyar na Ƙasa, Felix Morka, ya sanya wa hannu, APC ta ce waɗanda suka rasu suna kan hanyarsu ne ta zuwa Ƙaramar Hukumar Talata Mafara daga Gummi domin halartar ƙaddamar da kamfen ɗin zaɓen gwamnan jihar, lokacin da hatsarin ya afku.
Jam’iyyar ta bayyana lamarin a matsayin babban rashi na mambobi da magoya bayanta, tare da miƙa ta’aziyyarta ga Gwamnan Jihar ta Zamfara, Dauda Lawal, da iyalan mamatan, da gwamnatin jihar da kuma al’ummar Zamfara baki ɗaya.
Shugaban jam’iyyar na ƙasa, Farfesa Nentawe Yilwatda, ya bayyana mamatan a matsayin “mambobin jam’iyya masu kishinta, waɗanda jajircewarsu da halartar harkokin dimokuraɗiyya ba za a manta da su ba.”
“Bai kamata wani aiki ko harkar siyasa ya jawo asarar rayuka na bil’adama ba,” in ji shi.
Kana ya jajantawa waɗanda suka jikkata a hatsarin, tare da yi musu fatan samun cikakkiyar lafiya cikin gaggawa.
Haka kuma, APC ta yaba da matakin dage wani gangamin kamfe da aka shirya gudanarwa a Ƙaramar Hukumar Maru, domin nuna girmamawa ga waɗanda suka rasu da kuma nuna goyon baya ga iyalansu da ke cikin jimami.
Jam’iyyar ta bayyana matakin a matsayin “abin yabawa da ke nuna tausayi, haɗin kai da kuma girmama rayuwar bil’adama.”

















