Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Nijeriya (INEC) ta ce yanzu ingantacciyar rijistar masu zaɓe ta ƙasar ta ƙunshi fiye da mutane miliyan 100, bayan cire sunaye fiye da miliyan 1.6 na mutanen da suka mutu, waɗanda aka yi wa rajista fiye da sau ɗaya ko kuma ba su da inganci.
Shugaban hukumar INEC, Farfesa Joash Amupitan, ne ya bayyana hakan a ranar Laraba a Abuja, yayin wani taro da Kwamishinonin Zaɓe na jihohi 36 da Babban Birnin Tarayya, Abuja.
Ya bayyana cewa hukumar ta cire bayanan ne bayan gudanar da bincike ta hanyar amfani da na’urar tantance bayanan halittar jiki ta Automated Biometric Identification System, tare da tsarin doka na karɓar korafe-korafe da ƙalubalantar bayanan masu zaɓe.
A cewar Amupitan, fiye da mutane miliyan 11 ne suka yi rajista a cikin matakai uku na shirin ci gaba da rajistar masu zaɓe (CVR), wanda aka gudanar tun daga shekarar 2025. Ya ce an amince da rajistar fiye da miliyan 10.77 daga cikinsu, kuma an saka su cikin ingantacciyar rijistar.
Ya ce hukumar ta karɓi korafe-korafe kusan 311,000 a lokacin da aka bai wa jama’a damar duba rijistar tare da ƙalubalantar duk wani kuskure da suka gano. Daga cikin korafe-korafen, an tabbatar da cewa kusan 232,000 na gaskiya ne, kuma hukumar ta magance su.
Shugaban INEC ya kuma bayyana cewa ingantacciyar rijistar ta ƙunshi mutane 232,658 masu buƙata ta musamman, inda ya jaddada muhimmancin samar da wuraren kaɗa ƙuri’a masu sauƙin shiga da kayan tallafi da suka dace domin ba su damar shiga zaɓe.
A wani ɓangare kuma, hukumar ta zaɓi rumfunan zaɓe 17,676 domin gudanar da gwajin tantance masu zaɓe da kuma aika sakamakon zaɓe ta amfani da na’urar BVAS.
An shirya gudanar da gwajin a ranar Asabar, 28 ga Nuwamban 2026, a matsayin wani ɓangare na shirye-shiryen babban zaɓen ƙasar da za a yi a watan Janairun 2027.

















