Zanga-zangar da ta barke a Iran sakamakon tabarbarewar tattalin arziki da faduwar darajar kudin ƙasar ta rikide zuwa rikici mai tsanani, inda dubban rayuka suka salwanta, abin da ya jefa al’umma cikin alhini da fargaba game da makomar ƙasar.
Wata ƙungiyar kare haƙƙin ɗan’adam da ke da ofishi a Amurka ta bayyana cewa adadin mutanen da suka mutu a zanga-zangar Iran ya kai 4,029, yayin da sama da mutane 26,000 aka kama, kuma fiye da 5,800 suka jikkata.
Zanga-zangar ta fara ne daga Grand Bazaar a Tehran sakamakon faduwar darajar riyal da matsin tattalin arziki, sannan ta bazu zuwa faɗin ƙasar. Hukumomin Iran sun zargi Amurka da Isra’ila da goyon bayan masu tayar da ƙayar baya, yayin da Shugaban Amurka Donald Trump ya yi barazanar daukar mataki mai tsauri idan aka ci gaba da kashe masu zanga-zanga.














