Takaitaccen Labari: Barazanar da Gwamna Bago ke yi wa ‘yan jarida a Neja

Gwamna Bago na amfani da tsoro da barazana ga ‘yan jarida, inda ake kokarin dakile rahoto kan matsalolin tsaro a jihar. Gwamnati ta saba amfani da jami’an tsaro wajen cafke ko tsare ‘yan jarida, lamarin da ya kara nuna cewa tsaron jihar Neja na ci gaba da tabarbarewa. Wannan yanayi ya sa ‘yan jarida ke gudanar da aikinsu cikin fargaba da kuma tsoron rasa rayuwarsu.
1 Dec, 2025
Gwamnatin Sudan ta ce a shirye take ta yi aiki da MDD domin samar da zaman lafiya a ƙasar

Gwamnatin Sudan ta bayyana cewa a shirye take ta yi aiki kafaɗa da kafaɗa da Majalisar Ɗinkin Duniya domin samar da zaman lafiya da tsaro a ƙasar da kuma isar da kayayyakin agaji ga mabuƙata.
30 Nov, 2025
Matsalar man fetur a Mali ta ragu bayan sojoji sun yi wa tankokin mai rakiya a ƙasar

Tun daga watan Satumba, ‘yan ta’adda daga wata ƙungiya da ke da alaƙa da Al-Qaeda suka toshe hanyoyin jigilar mai zuwa wasu birane, lamarin da ya raunana tattalin arzikin ƙasar da ke Yammacin Afirka.
29 Nov, 2025
Kungiyar RSF ta Sudan ta kashe daraktan kamfanin dillancin labarai a Al Fasher

Ministan watsa labaran Sudan ya ce dakarun RSF ne suka kashe Taj Al-Sir Ahmed Suleiman a cikin gidansa tare da ɗan uwansa
29 Nov, 2025

Shugaban Guinea-Bissau ya tsere zuwa Senegal bayan sojoji sun yi masa juyin mulki

An ji ƙarar harbe-harbe a kusa da fadar shugaban ƙasar Guinea-Bissau- Rahotanni

Hukumomi a Nijar sun kama CFA fiye da miliyan 1.7 da dubban miyagun ƙwayoyi a jihar Tahoua

“‘Yan’uwa ‘yan Sudan” suna son Turkiyya ta sa hannu a ƙoƙarin samar da zaman lafiya: Erdogan

Burhan ya yi watsi da tayin Amurka na tsagaita a Sudan, ya ce shi ne ‘mafi muni a tarihi’
22 Nov, 2025
Yaƙin Sudan: Fiye da yara 20 sun mutu sakamakon tsananin rashin abinci a cikin wata guda
Mutuwar yara 23 a yankin Kordofan ta nuna yadda ake da matuƙar buƙatar kayan jinƙai a ƙasar da ke arewa maso gabashin Afirka, inda yunwa ke ƙaruwa bayan fiye da watanni 30 na yaki.

22 Nov, 2025
An ƙaddamar da taron shugabannin ƙasashen G20 a Afirka ta Kudu
A yayin wannan taron wanda jigonsa zai kasance ‘hadin kai, daidaito da ɗorewa’, shi ne taron G20 na farko da aka taba gudanarwa a nahiyar Afrika, kuma zai mayar da hankali kan sassauta bashi ga ƙasashe masu ƙaramin ƙarfi.

20 Nov, 2025
Mutane 70 sun ɓace bayan jirgin ruwa ɗauke da mutum 120 ya kife a DRC
Kafofin watsa labarai na cikin gida sun ce jirgin yana ɗauke da kimanin mutum 120, kuma daga cikinsu kimanin 50 kawai aka iya cetowa kawo yanzu.

18 Nov, 2025
Sabon Alƙalin Alƙalan Ghana Baffoe-Bonnie ya fara aiki
Ranar Alhamis ne dai majalisar dokokin ƙasar ta amince da sunan alƙalin da shugaban ƙasar ya miƙa mata a matsayin sabon alƙalin alƙalan ƙasar.

17 Nov, 2025
Za a ƙara farashin man fetur a Ghana
Bayanai daga masana’natar mai sun nuna cewa za a kara farashin mai kama daga kashi 1.18 cikin 100 zuwa kashi 3.54 cikin 100, inda za a sayar da ko wace lita ɗaya ta mai kan kuɗi GH¢13.15 (wato naira 1731.90 kuɗin Nijeriya).

17 Nov, 2025
Ruftawar mahaƙar ma’adanai ta yi ajalin aƙalla mutum 32 a DRC
Wata gada ta rufta a wata mahaƙar ma’adinai na kobolt a kudu maso gabashin Jamhuriyar Dimokraɗiyyar Kongo inda ta kashe aƙalla masu haƙar ma’adinai 32, kamar yadda wani jami’in gwamnati a yankin ya bayyana ranar Lahadi.

16 Nov, 2025
An samu rahotanni 32 na yi wa ‘yan mata fyade bayan RSF ta ƙwace birnin Al Fasher – Likitoci
Wasu daga cikin ‘yan matan an yi musu fyaɗe a cikin Al Fasher bayan RSF ta ƙwace garin, yayin da wasu aka ci zarafin su a lokacin da suke ƙoƙarin tserewa zuwa garin Tawila da ke maƙwabtaka, in ji Ƙungiyar Likitocin Sudan.

16 Nov, 2025
Mutum huɗu sun rasu bayan jiragen ruwa biyu na ‘yan ci-rani sun kife a gaɓar tekun Libya
Ƙungiyar bayar da agaji ta Libyan Red Crescent ta ce an tura ma’aikatan agajin gaggawa zuwa wurin don ceto waɗanda suka tsira da ɗauko gawawwakin waɗanda suka mutu, da kuma ba da kulawa.

15 Nov, 2025
AfDB zai ba Nijar CFA biliyan 98.7 domin magance matsalar ruwa ta shekara 70 a Zinder
Firaiministan Nijar Ali Mahaman Zeine ya bayyana girman matsalar ruwa a wannan yankin wadda ya ce matsala ce tun ta zamanin mulkin mallaka, ya kuma ce ko tashar samar da ruwa ta farko ta Aroungouza wadda aka gina a 1955 ba ta taɓa magance matsala.

14 Nov, 2025
MDD ta yi gargaɗi kan ƙazancewar yaƙin Sudan, ta yi kira kan barin shigar da kayan agaji
Kusan mutum 100,000 suka rasa muhallansu a Al Fasher da ƙauyukan da ke kewaye tun bayan da RSF ta ƙwace iko da yankin.


