Sojin Sudan sun yi wa ‘yan ta’adda mummunar ɓarna bayan hari a Al Fasher

Rundunar sojin Sudan tare da haɗin gwiwar ‘yan sanda sun tare maharan inda suka kashe da yawa daga cikinsu.
20 Oct, 2025
Nnamdi Kanu: ‘Yan sanda a Abuja sun tarwatsa masu zanga-zangar neman a saki jagoran IPOB na Nijeriya

‘Yan sandan Nijeriya sun harba hayaki mai sa hawaye a ranar Litinin tare da mamaye manyan hanyoyin babban birnin Abuja don dakatar da zanga-zangar adawa da ci gaba da tsare shugaban ‘yan ta’addar aware na Biafra IPOB Nnamdi Kanu.
20 Oct, 2025
Dakarun tsaron Nijar sun kashe ‘yan ta’adda a Jihar Dosso

Rahotanni daga Jamhuriyar Nijar sun ce lamarin ya auku ne a lokacin da wasu ‘yan ta’adda ɗauke da makamai bisa babura suka yi wa dakarun tsaron ƙasar kwanton-ɓauna da bai yi nasara ba.
20 Oct, 2025
A shirye Sojojin Sudan suke domin tattaunawa don dawo da zaman lafiya: Burhan

Kalaman na Burhan na zuwa ne gabanin fara taron ƙasashen Amurka da Saudiyya da Masar da Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa wanda za a yi a birnin New York domin lalubo mafita kan yadda za a kawo ƙarshen yaƙin Sudan.
19 Oct, 2025

Dangantaka tsakanin Turkiyya da Afirka ta shiga wani sabon babi mai ƙarfi – Kwamishinar Ƙungiyar AU

Hotuna: Dubunnan mutane sun halarci jana’izar madugun ‘yan adawa na Kenya Odinga

Sojojin da suka yi juyin mulki a Madagascar sun ce a shirye suke su tattauna da Tarayyar Afirka

Ƙungiyar AU ta dakatar da Madagascar daga cikinta sakamakon juyin mulki a ƙasar

Odinga: Ruto ya ayyana makokin kwana bakwai a Kenya don jimamin mutuwar tsohon firaministan ƙasar
14 Oct, 2025
Issa Tchiroma Bakary ya yi iƙirarin lashe zaɓen shugaban ƙasar Kamaru
Ɗan takarar jam’iyyar hamayya Issa Tchiroma Bakary ya yi kira ga Paul Biya ya amsa shan kaye ko da yake gwamnati ba ta ce uffan ba game da iƙirarin da ya yi na lashe zaɓen shugaban ƙasar Kamaru.

12 Oct, 2025
‘Yan Kamaru na kaɗa ƙuri’a a zaɓen da Paul Biya ke neman wa’adi na takwas
’Yan takara 13 ne suke neman maye gurbin Shugaba Biya ciki har da wasu da suka taɓa kasancewa na hannun damansa a shekarun baya.

11 Oct, 2025
Jirgi maras matuƙi na RSF ya kashe mutum 30 birnin Al-Fasher na Sudan
Kwamitin ‘yan gwagwarmaya na Al-Fasher ya ce jirgin na RSF ya kai harin ne a sansanin ‘yan gudun hijira na Dar al-Arqam da ke cikin harabar wata jami’a inda aƙalla mutum 30 suka rasu.

10 Oct, 2025
Burkina Faso ta ƙi karɓar mutanen da aka kora daga Amurka
Matakin na Burkina Faso ya zo ne a daidai lokacin da ofishin jakadancin Amurka da ke Ouagadougou babban birnin ƙasar ya dakatar da ayyukan biza, matakin da gwamnatin Traore ta kira ”bita-da-ƙulli”.

8 Oct, 2025
Shugaban Kamaru Biya ya yi fitowar ba-zata, ya ƙaddamar da yaƙin neman zaɓe
A baya bayan nan ba a ganin Shugaban Paul Biya a wajen yaƙin neman zaɓe, kasancewar bai jima da dawowa daga Switzerland ba, inda ya shafe kwanaki dama.

8 Oct, 2025
ICC ta tuhumi shugaban ‘yan bindiga na Sudan Ali Kushayb da laifukan keta hakkin bil’adama
Tuhumar ce hukuncin ICC na farko da ya shafi rikicin Darfur kuma ana sa rai zai zama misalin yin adalci a ɗaya daga cikin rikice-rikicen jinƙai mafiya daɗewa a Afirka.

8 Oct, 2025
Sojojin Sudan sun sake ƙwace muhimman wurare daga dakarun RSF a El-Fasher
Wata sanarwa da rundunar sojin Sudan ta fitar ta ce dakarunta sun kai farmaki a wurare daban-daban da ke hannun mayaƙan RSF a El-Fasher inda suka sanya su yin asarar dakaru da kayayyakin aiki.

6 Oct, 2025
Hare-haren RSF sun kashe gomman mutane a yankin Darfur na Sudan: Likitoci
Cibiyar Likitocin Sudan (Sudan Doctors Network) ta ce cikin waɗanda suka jikkata akwai yara bakwai da mace mai juna biyu, a harin da aka kai unguwannin zama na Al Fasher, babban birnin Arewacin Darfur da ke yammacin Sudan.

6 Oct, 2025
Ayyukan da sojojin Nijar suke yi a yankin Tillaberi sun fara tasiri: Shugaba Tiani
Shugaba Tiani ya bayyana haka ne a lokacin da ya kai ziyara Jihar Tilleberi inda ya yi rangadin dakarun da ke jihar wadda ke fama da matsalar tsaro.

5 Oct, 2025
RSF ta kai hari da jirgi maras matuƙi na ƙunar baƙin-wake kan fararen-hula a Sudan – Sojoji
Rundunar Sojin Sudan ta zargi ƙungiyar RSF da kai hari kan fararen-hula a Kordofan ta Arewa da ke kudancin Sudan ta hanyar amfani da jirgi maras matuƙi.


