5 Oct, 2025

An yanke wa wani mutum hukuncin kisa kan zagin shugaban ƙasar Tunisia a Facebook

Lauyan wanda aka yanke wa hukuncin ya ce mutumin ba shi da wani cikakken ilimi sannan abubuwan da ya rinƙa wallafawa a Facebook akasari kwafo su ya rinƙa yi daga wasu shafuka domin jawo hankalin gwamnati kan mawuyacin halin da jama’ar ƙasa ke ciki.

tunisia protest 42830

3 Oct, 2025

Jami’an tsaron Nijar sun kama hodar ibilis ta CFA biliyan 2.6

Jami’an tsaron sun kama wani direban mota ɗan Nijeriya ɗauke da sunƙi 47 na hodar ibilis da nauyinsu ya kai kilo 51.7, waɗanda ya ɗauko tun daga Ghana zai kai su Yamai.

6a534361639dd10d730f57dc9465f1be483351e6e021cd331917e555cfdcb18c

3 Oct, 2025

‘Yan bindiga sun kashe aƙalla mutum 14 a sansanin ‘yan gudun hijira na DR Kongo

Harin da aka kai a yankin Djugu ya afku ne a ranar Alhamis a daidai lokacin da mutanen da suka rasa matsugunansu daga yankin Rhoo ke kan hanyarsu ta zuwa gonakinsu a ƙauyukan da ke kewaye, a cewar rahoton.

2c3175c686672b09d1a4faa17abb6f1ac21fbb8638b5e48a200282c4cecfe7c9

2 Oct, 2025

Zanga-zangar neman ingantaccen ilimi da kiwon lafiya ta matasan Maroko ta shiga kwana na huɗu

Haɗakar gwamnati ta bayyana amincewarta da tattaunawa da matasan cikin hukumomi da wurare na gwamnati domin samun mafita na gaske.

35ea9db82bfc3e7d796d2faf426f845e9058846d2de787165d2a00d5b1f10dc5

1 Oct, 2025

DRC ta yanke wa tsohon Shugaba Joseph Kabila hukuncin kisa

Wata kotun sojoji a Jamhuriyar Dimokuradiyyar Kongo ta yanke wa tsohon Shugaban kasar Joseph Kabila hukuncin kisa a bayan idonsa, bisa samunsa da laifuka, ciki har da laifukan yaƙi.

2025 05 28t095600z 1 lynxnpel4r0e4 rtroptp 3 congo security kabila main

28 Sep, 2025

UNGA 80: Nijar ta ce dole Faransa ta ‘ɗauki alhakin laifukan da ta yi’ mata tun daga shekarar 1899

Firaministan Jamhuriyar Nijar Ali Lamine Zeine, a jawabinsa a Babban Taron MDD, ya zargi Faransa da “haddasa rashin zaman lafiya” a ƙasashen Sahel inda take ɗaukar nauyin “‘yan ta’adda” tare da tunzura rikici a ƙasarsa da maƙotanta.

b7005a5867bcc55ccc6015bb1de30f264b0e5dc55f272c49944f7200bc69e0b0

27 Sep, 2025

Amurka ta cire takunkumin biza kan Ghana bayan cim ma yarjejeniya kan karɓar waɗanda Trump ke kora

A farkon watan nan ne Shugaban Ghana John Dramani Mahama ya sanar da cewa ƙasarsa za ta rinƙa karɓar ‘yan Yammacin Afirka da Gwamnatin Trump ta kora.

1758967856783 jwxn8e 7c9af3516db6a5144fea5acaac35e0433e3909d42b0c636697c0e540efc05e78

26 Sep, 2025

Nijar ta ce tana son ta gina injunan makamashin nukiliya biyu tare da Rasha

Nijar ɗaya ce daga cikin ƙasashen Afirka da Rasha take ƙarfafa dangantaka da su a fannoni ciki har da na tsaro.

2025 06 11t135527z 879152783 rc20p6a4qdd6 rtrmadp 3 europe power nuclear

24 Sep, 2025

Shugaba Mahama ya gabatar da sunan Paul Baffoe-Bonnie a matsayin alƙalin alƙalan Ghana

Kazalika sanawar ta ce Mai Shari’a Baffoe-Bonnie ya ba da gudunmawa mai yawa a fannin shari’ar Ghana.

5921d8d40f9c7b66e4d8882b32f3d83c0367c79d9ef40ccba86893cd4853e517

24 Sep, 2025

IAEA: An zaɓi Nijar a kwamitin gudanarwa na hukumar kula da makamashin nukiliya ta duniya

Kwamitin mai mambobi 35 na ɗaya daga cikin manyan kwamitoci da suke yanke hukunci da sa ido kan batun nukiliya tare da amincewa da kasafin kuɗi da tsara manufofin duniya kan makamashin nukiliya.

20663762 0 0 760 428
Ana lodawa...