‘Yan bindiga sun kashe mutum uku da sace matan aure a Nijar

‘Yan bindigar sun kai hare-hare biyu a yankin Maradi na Jamhuriyar Nijar inda suka kashe mutum uku tare da sace matan aure da ‘yan mata.
1 Aug, 2025
Gwamnatin Ghana za ta fara cin tarar direbobin da ke lodi fiye da ƙima Cedi 50,000

Gwamnatin Ghana ta ce hanyoyin ƙasar da dama sun lalace sakamakon lodi fiye da ƙima da ake yi wa motoci wanda hakan ya sa za a ƙara yawan tarar da ake cin direbobin da suka saɓa doka daga Cedi 5,000 zuwa Cedi 50,000.
1 Aug, 2025
MDD ta ce yara 80,000 na cikin haɗarin kamuwa da cutar kwalara a Yammaci da Tsakiyar Afirka

Ɓarkewar annobar kwalara a Jamhuriyar Dimokradiyyar Kongo da Nijeriya ya jawo fargabar cewa za a iya samun yaɗuwar cutar a tsakanin ƙasashe maƙwabta, in ji Hukumar Majalisar Dinkin Duniya
31 Jul, 2025
An samu mace-macen farko da ke da alaƙa da Mpox a Ghana yayin da cutar ke yaɗuwa cikin sauri

An tabbatar da ƙarin mutane 23 sun kamu da cutar a makon jiya, wanda ya kawo adadin waɗanda suka kamu da cutar zuwa 257 tun lokacin da aka fara gano ta a Ghana a watan Yunin 2022.
29 Jul, 2025

Nijar da Rasha sun rattaba hannu kan yarjejeniyar makamashin nukiliya da haƙar yuraniyom

Amurka ta dakatar da ayyukan bayar da biza a ofishin jakadancinta na Nijar

Senegal ta haramta amfani da babura a kusa da iyakarta da Mali

Mutum fiye da 1.3M sun koma gida Sudan, MDD na buƙatar ƙarin tallafi

Nijar ta ƙaddamar da bincike kan dutsen meteorite da aka tsinta a ƙasarta aka sayar a Amurka
21 Jul, 2025
Shugaba John Mahama na Ghana ya dakatar da shugaban hukumar kula da tsaron intanet ta ƙasar
An dakatar da Mista Divine Selasi Agbeti kan zargin amfani da soja a matsayin dogari musamman a wuraren da ake taro ba tare da izini ba.

20 Jul, 2025
Jami’an tsaron Nijar sun kama mutum bakwai da ake zargi da tallafa wa ta’addanci a yankin Tillaberi
Jami’an Operation Niya da ke Nijar sun samu nasarori a farmaki daban-daban da suka kai, daga ciki har da masu haɗa bama-bamai da masu sayar wa ‘yan ta’adda dabbobin sata da masu yi wa ‘yan ta’adda fasa-ƙwaurin man fetur.

19 Jul, 2025
Jamhuriyyar Kongo da ‘yan tawayen M23 sun cim ma yarjejeniya domin dakatar da rikici a gabashin DRC
An cim ma yarjejeniyar ne bayan ɓangarorin biyu sun shafe watanni uku suna tattaunawa a Doha babban birnin Qatar.

17 Jul, 2025
Faransa za ta miƙa sansanin sojinta na ƙarshe da ke Senegal
Sojojin Faransa kusan 350 za su bar ƙasar da ke Yammacin Afirka a ranar Alhamis inda Faransar za ta mika Camp Geille, wanda shi ne sansaninta mafi girma a ƙasar, tare da filin jirgin sama na Dakar.

15 Jul, 2025
Dakarun RSF ‘sun kashe fararen-hula kimanin 300’ a yankin da suke da karfi
Harin da dakarun RSF suka kai “bashi da wata manfa ta soji” a Arewacin Kordofan, a cewar masu fafutuka.

13 Jul, 2025
Dakarun RSF na Sudan sun kashe mutum 11, har da yara a cikinsu
Yara uku na daga cikin mutum 11 da dakarun RSF suka kashe sannan suka jikkata aƙalla 31, daga ciki har da mata tara, wasunsu na da juna biyu, kamar yadda likitoci suka tabbatar.

12 Jul, 2025
MDD ta dakatar da bayar da tallafin abinci a Yammaci da Tsakiyar Afirka
Shirin Samar da Abinci na Majalisar Ɗinkin Duniya (WFP) ya ce yana buƙatar dala miliyan 494 domin gudanar da aikin ciyarwa amma kuɗinsa sun ƙare sakamakon rage bayar da tallafin da Amurka ta yi.

11 Jul, 2025
Paul Biya ya sanar da cewa za a yi zaɓen Shugaban Ƙasa a Kamaru a Oktoban 2025
Shugaban Paul Biya mai shekara 92, wanda shi ne Shugaban Ƙasa mafi yawan shekaru a duniya, bai yi magana kan ko zai sake tsayawa takara ba.

11 Jul, 2025
Mutum huɗu a Afirka da arzikinsu ya fi rabin na nahiyar – Oxfam
Oxfam ta ce cewa manufofin gwamnati sun fi takura wa talakawa kuma ta zargi “tsauraran” manufofin Asusun Ba da Lamuni na Duniya da ƙara janyo rashin daidaito.

2 Jun, 2025
‘Yan ta’adda sun ƙwace sansanin soji a Mali, sun ‘kashe sojoji fiye da 30’
Tun farkon watan Mayu, an ruwaito cewa fiye da sojoji 400 sun rasa rayukansu a hannun ‘yan bindiga a sansanoni da garuruwa a Mali, Nijar, da Burkina Faso.



