Ghana ta kama ‘yan kasashen waje fiye da 2,000 da suka shiga kasar ba bisa ka’ida ba

Yawancin waɗanda aka kama a samamen sun fito ne daga Burkina Faso da ke maƙwabtaka, wadda ke ƙarƙashin mulkin soja, da kuma daga Togo. Wasu daga cikin su sun fito ne daga nesa kamar Najeriya.
17 May, 2025
Sojoji sun ‘ɗauke’ tsohon Firaiministan Chadi Succes Masra

An tafi da Succes Masra, wanda ke jagorantar ‘yan adawa a Chadi zuwa wani wuri da ba a san ko ina ba ne, in ji jam’iyyarsa.
16 May, 2025
Gwamnatin Nijar ta haramta achaɓa a wasu sassan yankin Dosso

Gwamnan yankin Dosso ya ce babban dalilin saka haramcin shi ne daƙile zirga-zirgar ‘yan ta’adda waɗanda suke amfani da babura domin sufuri.
16 May, 2025
Mayakan RSF sun kai harin da ya katse lantarki a Khartoum

Katsewar lantarki ta dakatar da ayyuka, da ta’azzara wahalhalun da mutane ke sha, in ji hukumar lantarki ta kasar.
15 May, 2025

Hajjin 2025: Jirgin farko dauke da alhazai 363 ‘yan Nijar ya tashi zuwa Saudiyya

Afirka ta Kudu za ta dukaka kara kan wanke fasto dan Nijeriya daga zargin fyade

Shugaban Ghana nemi kasashen Afirka su tsayar da manufa daya gabanin taron G20

Aljeriya ta kori jami’an leƙen asirin Faransa biyu daga ƙasarta kan kama su da fasfon bogi

Ambaliyar ruwa ta kashe mutum 62 a Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Kongo
11 May, 2025
Gwamnatin Nijar ta haramta fitar da dabbobi daga ƙasar gabanin Sallar Layya
Gwamnatin ta Nijar ta haramta fitar da shanu da raguna da awaki da raƙuma gabannin Babbar Sallah domin daƙile irin yadda farashinsu ke tashin gwauron zabi.

9 May, 2025
Yakin Sudan: Jiragen yaki marasa matuka sun yi luguden wuta a Port Sudan
Sabbin hare-haren sun sanya tsoron samun karancin man fetur da tabarbarewar rikicin jinkai.

8 May, 2025
Rikici a Sudan ta Kudu ya hana kai kayan agaji ga yara 60,000 da ke fama da tsananin yunwa
A tsakiyar watan Afrilu, an tilasta wasu jiragen ruwa dauke da tan 1,000 na abinci da kuma sauran kayan abinci masu gina jiki da suka nufi jihar Upper Nile koma wa saboda rashin tsaro, in ji WFP da UNICEF.

8 May, 2025
Mayaƙan RSF sun ƙaddamar da sabbin hare-hare a gabashi da kudancin Sudan
RSF ta kai sabbin hare-haren ne a babban sansanin sojin ruwa da ke wajen Port Sudan, da kuma wasu daga cikin defo-defo na fetur a kudancin birnin Kosti, kamar yadda wata majiyar soji da ta buƙaci a sakaya sunanta ta bayyana.

7 May, 2025
Tawagar IMF ta gana da Firaministan Nijar game da garambawul kan tattalin arzikin ƙasar
“Nijar za ta iya dogaro kan IMF saboda muna da dangantaka mai kyau, musamman ta ɓangaren samar da rance da kuma juriya na ɗorewa [na lamurra],” in ji jami’in na IMF.

6 May, 2025
Sudan ta yanke alaƙar diflomasiyya da ƙasar Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa
Gwamnatin sojojin Sudan ta yanke alaƙar diflomasiyya da Lamuran ƙasar Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa, tana bayyana kasar a matsayin “mai yin katsalandan.”

6 May, 2025
Jirgin ruwa na biyu ɗauke da kayan tallafi daga Turkiyya ya isa Sudan ana tsaka da yaƙi
Daga abinci zuwa sauran kayan bukatun yau da kullum – tallafin jinƙai na Turkiyya na ci gaba da zuwa yankuna, tana tunatar da cewa rikici na iya raba kawuna, amma tausayi na hade su.

6 May, 2025
An ji ƙarar fashewar bama-bamai a birnin Port Sudan
An shaida fashewar bama-bamai da tashin gobara a babban birnin ƙasar Port Sudan yayin da birnin ke fama da yaƙin basasa.

5 May, 2025
An jefi shugaban Kenya William Ruto da takalmi yana tsaka da jawabi
Wani gajeren bidiyo da ke yawo a shafukan sada zumunta ya nuna yadda takalmin ya sami shugaban a kafaɗarsa ta hagu a lokacin da yake gudanar da jawabi.

4 May, 2025
RSF ta kai hari birnin Port Sudan da jirage marasa matuƙa
A karon farko, dakarun RSF sun kai hari wuraren da soji ke iko da su a Port Sudan da jirage marasa matuƙa masu ƙunar-baƙin-wake, wanda wata alama ce da ke nuna wani sabon salo da yaƙin ke ɗauka wanda aka shafe fiye da shekara biyu ana gwabzawa



