Ƙoƙarin gano hanyoyin dakatar da yaƙin Ukraine na ci gaba da faɗaɗa, inda ake gudanar da muhimman tattaunawa a Florida da Beijing, yayin da Shugaba Putin na Rasha yake a India domin ƙarfafa alaƙarsa da ɗaya daga manyan abokan huldarsa.
Fadar White House ta tabbatar da cewa wakilin musamman na Shugaba Trump, Steve Witkoff, zai gana da masu shiga tsakani na Ukraine a yau Alhamis, domin tattauna martanin Rasha kan shirin zaman lafiya da Amurka ke goyon baya.
Witkoff zai kuma gabatar wa Trump da rahoton zantukansa da Putin a Moscow, inda Putin ya bayyana cewa Rasha ba za ta amince da wasu muhimman sassa na shirin zaman lafiyar ba. Haka nan Ukraine ta ƙi amincewa da mika duk yankunan da Rasha ke nema a matsayin sharadin kulla sulhu.














