Gwamnatin Amurka ta sanya takunkumai kan wasu ‘yan Nijeriya 18 da wasu ƙungiyoyi bisa zargin alaƙa da ta’addanci, laifukan intanet da safarar miyagun ƙwayoyi. Matakin ya zo ne yayin da Washington ke ci gaba da ƙarfafa haɗin kai da Nijeriya a fannin tsaro da yaƙi da masu tsattsauran ra’ayi.
Ofishin kula da kadarori na ƙetare (OFAC) ya ayyana sunayen wasu a jerin SDGT da CYBER2 da SDNTK. Daga cikin waɗanda aka ambata akwai mutanen da ake zargin suna da alaƙa da Boko Haram, ISWAP da Ansaru, tare da wasu da ake zargi da damfara ta intanet.
Amurka ta ce takunkuman na nufin hana zirga-zirgar kuɗi da duk wata hulɗa da za ta iya tallafa wa ayyukan ta’addanci ko laifuka na ƙasa da ƙasa. Haka kuma an ambaci wasu da ake zargi da safarar miyagun ƙwayoyi a matakin duniya.
Matakin na daga cikin jerin manufofin Amurka na daƙile barazanar tsaro, laifukan intanet da safarar ƙwayoyi, yayin da ake sa ran ƙarin haɗin kai da ƙasashen Afirka wajen magance waɗannan matsaloli.
Majiyar Labari: TRT HAUSA














