Jihar Neja na ci gaba da fuskantar mawuyacin hali yayin da hare-haren ‘yan bindiga suka tilasta wa dubban iyalai barin gidajensu. Gwamna Umaru Mohammed Bago ya bayyana cewa fiye da mutum 300,000 ne aka raba da muhallansu a ƙananan hukumomi sama da goma sakamakon hare-haren da ba su tsaya ba.
Jihar na daga cikin wuraren da matsalar tsaro ta fi ƙamari a arewacin Nijeriya, inda ‘yan bindiga ke kai farmaki kan ƙauyuka, suna kashe mutane da garkuwa da su ciki har da ɗalibai. Wannan lamari ya katse hanyoyin rayuwa, ya hana manoma zuwa gonaki, sannan iyaye da dama sun fara jin tsoron tura ‘ya’yansu makaranta.
Da yake magana da manema labarai a Minna bayan karɓar tallafin jin ƙai daga gwamnatin tarayya, Gwamna Bago ya ce har yanzu ana tattara sahihan alkaluma saboda hare-haren na ci gaba. Ya jaddada cewa gwamnatinsa na aiki tare da hukumomin tsaro da gwamnatin tarayya domin dawo da zaman lafiya.
Gwamnan ya nuna fata cewa sabbin matakan tsaro za su bai wa waɗanda aka raba da gidajensu damar komawa muhallansu da kuma ci gaba da rayuwarsu yadda ta saba.














