Nijeriya

Amurka ta tura jirage marasa matuƙa Nijeriya don tattara bayanan sirri kan ‘yanta’adda

Daraktan watsa labarai na Hedkwatar Tsaron Nijeriya ya tabbatar cewa Amurka na amfani da wani sansanin sojin ƙasar da ke Jihar Bauchi.

Newstimehub

Newstimehub

21 Mar, 2026

1774089253967 5509gi acd12b335d432fb0a9d77e0793c7eb441ddd17b3fa3953782049a57cd75e85e2

Amurka ta tura jirage marasa matuƙa samfurin MQ-9 da dama zuwa Nijeriya tare da dakaru 200 domin bayar da horo tare da tattara bayanan sirri don bai wa sojojin ƙasar waɗanda suke yaƙi da ta’addanci a arewacin ƙasar, in ji wasu jami’ai na gwamnatocin Amurka da Nijeriya a hirarsu da kamfanin dillancin labarai na Reuters.

Ba a haɗa dakarun da takwarorinsu na Nijeriya da ke filin yaƙi sannan jirage marasa matuƙan suna tattara bayanan sirri kuma ba sa kai hare-hare ta sama, a cewar jami’an ƙasashen biyu.

An tura sojojin ne bayan wani hari da Amurka ta kai a Jihar Sokoto da Kwarai a ƙarshen shekarar 2025 waɗanda ta yi iƙirarin kashe ‘yanta’adda da dama a ƙoƙarin da ta ce tana yi na kawar da ta’addanci daga Yammacin Afirka.

Wani jami’in tsaron Amurka ya ce an tura jirage marasa matuƙan tare da dakarun ƙasar domin bayar da horo tare da tattara bayanan sirri kamar yadda gwamnatin Nijeriya ta buƙata.

“Muna kallon wannan a matsayin barazanar tsaro da ta shafe mu duka,” in ji jami’in.

‘Ba za su je filin yaki ba’

Manjo Janar Samaila Uba, daraktan watsa labarai na Hedkwatar Tsaron Nijeriya, ya tabbatar cewa Amurka na amfani da wani sansanin sojin ƙasar da ke Jihar Bauchi.

“Wannan tallafi zai taimaka wajen bunƙasa sabuwar alaƙa ta tsaro tsakanin Amurka da Nijeriya, ta hanyar bayan da bayanan sirri ga kwamandojinmu da ke filin yaƙi,” kamar yadda ya shaida wa Reuters.

“Abokan aikinmu na Amurka ba za su je fiin yaƙi ba, za su bari dakarun Nijeriya su yi hakan.”

Uba ya ce ba a san tsawon lokacin da dakarun Amurka za su kwashe suna gudanar da aikinsu a Nijeriya ba, yana mai cewa yarjeniyoyin da ƙasashen biyu suka ƙulla su ne za su tantance hakan.