Nijeriya Tsaro

Amurka za ta tura sojojinta 200 Nijeriya

Amurka za ta tura dakaru 200 Najeriya domin horas da sojoji da ba da taimako na fasaha a yaƙin da ake da ’yan ta’adda.

Newstimehub

Newstimehub

11 Feb, 2026

ac73b79f621b79f31560f34de26e31c06b895fae134ed8b512765f9a4a244d41

Amurka na shirin tura dakaru 200 zuwa Najeriya domin horas da sojojin ƙasar da kuma ba da taimako na fasaha a yaƙin da ake da ƙungiyoyin ’yan ta’adda. Jami’an tsaro sun ce dakarun za su yi aiki ne tare da tawagar sojin Amurka da ke ƙasar, inda za su mayar da hankali kan horo, shawarwari da tallafin fasaha, ciki har da daidaita ayyukan hare-hare ta sama da ƙasa.

Rundunar Afirka ta sojin Amurka ta tabbatar da shirin, wanda ke nuna ƙarin kusanci a alaƙar tsaro tsakanin ƙasashen biyu.

Shirin na zuwa ne a daidai lokacin da ake ci gaba da muhawara kan matsalar tsaro a Najeriya. Shugaban Amurka Donald Trump ya taɓa bayyana damuwa kan rikice-rikicen da ke ƙasar, yayin da gwamnatin Najeriya ta yi watsi da zarge-zargen da ke cewa ana yi wa Kiristoci kisan gilla.

Jami’an Amurka sun kuma jaddada cewa hare-haren ’yan ta’adda sun shafi al’ummomi daban-daban, ba tare da bambancin addini ba.

Majiyar Labari: TRT HAUSA