Turkiyya

An karrama sojojin Turkiyya da suka yi shahada a hatsarin jirgin sama a iyakar Azerbaijan da Georgia

Bayan bikin karramawar an aika da gawarwakin sojojin zuwa garuruwansu don yi musu jana’iza.

Newstimehub

Newstimehub

14 Nov, 2025

0ab1be88b4163dfd029f0175c637e40d9970ebb61388f8b4ac04a3d64e244aad

An gudanar da bikin bankwana a ranar Juma’a a sansanin sojojin sama na Murted da ke babban birnin Ankara ga sojojin Turkiyya da suka rasa rayukansu a hatsarin jirgin saman soja da ya afku a iyakar kasashen Azerbaijan da Georgia.

Jirgin saman rundunar sojin saman Turkiyya samfurin C-130 ya fado a kusa da kan iyakar Azerbaijan da Georgia a ranar 11 ga Nuwamba, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar dukkan ma’aikata 20 da ke cikin jirgin.

Bikin ya fara da shiru na ɗan lokaci, karatun Alqur’ani Mai Tsarki da kuma addu’o’i ga sojojin da suka yi shahada.

Bayan an karanta takardun shaidar aikinsu, an kai akwatunan gawarwakin sojojin zuwa jiragen sama na soja domin a kai su garuruwansu don a yi musu jana’iza.

An gudanar da bikin ne tare da halartar shugaban Majalisar Dokokin Turkiyya Numan Kurtulmus, Ministan Tsaron Kasa Yasar Guler, Ministar Harkokin Iyali da Zamantakewa Mahinur Ozdemir Goktas, ‘yan majalisa, manyan kwamandojin sojojin Turkiyya.

Sai kuma gwamnan Ankara Vasip Sahin, kwamandan rundunar sojin sama ta Azerbaijan Manjo Janar Namig Islamzade, jakadan Azerbaijan a Ankara Reshad Mammadov, da iyalan sojojin.

Shugaban ƙasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya mika sakon ta’aziyyarsa ga iyalan sojojin, yana mai bayyana matuƙar baƙin cikinsa game da wannan mummunan rashi da kuma yin addu’o’i gare su.