Ma’aikatar Sufuri da Samar da Ababen More Rayuwa ta Turkiyya ta sanar cewa a ranar Lahadi 16 ga Oktoban 2025, Turkiyya za ta gudanar da bikin bayar da aikin assasa layin sadarwa na 5G wanda za a kaddamar da fara amfani da shi a shekarar 2026 mai zuwa.
Ana sa ran matakin na 5G zai karfafa hanyoyin sadarwa na kasar, da bayar da damar hanzarta aika bayanai da karfafa hanyoyin sadarwa.
A ranar 16 ga watan Agusta ne wata doka ta Shugaban Ƙasa da aka buga a Jaridar Gwamnati ta fara gudanar da shirin a hukumance, inda ake sa ran za a gudanar da bikin bayar da kwangilar aikin a ranar 16 ga Oktoba, a cewar ma’aikatar.
Shirin wani bangare ne na manyan tsare-tsare don bunkasa fasahohin da suka kunno kai kamar su Kirkirarriyar Basira (AI), manyan bayanai, manhajoji, motoci masu aiki da kansu, da dabarun kera kayayyaki, a cewar wani rahoto na Hukumar Fasahar Sadarwa da Bayanai (BTK).
Masana’antu daban-daban za su amfana da aikin
Gwajin da aka gudanar a dakunan gwaje-gwajen a bara ya nuna saurin layin sadarwa na 5G na gigabits 7.5 a sakan daya, yayin da ainihin hanyoyin sadarwa ke da saurin gigabits 4.7 a sakan daya.














