Rahotanni daga majiyoyin tsaro sun tabbatar da cewa an kashe sojoji tara sannan wasu suka jikkata bayan ayarinsu ya taka nakiya kafin ’yan ta’adda su kai musu harin kwanton-bauna a yankin Bindundul, kusan kilomita 20 daga Kareto a Jihar Borno.
Majiyoyi sun bayyana cewa ’yan ISWAP — reshen kungiyar IS da ke Yammacin Afirka — ne suka kitsa harin, yankin da suka dade suna cin karensu babu babbaka tare da kafa shingayen bincike. Wani jami’i daga rundunar agaji ya ce motar soja mai sulke ta lalace sakamakon fashewar nakiyar, sannan aka rika bude wuta ga sojojin.
Sojojin sun kasance cikin tafiya daga Maiduguri zuwa Damasak lokacin da lamarin ya faru. A halin yanzu rundunar sojin Najeriya ba ta fitar da cikakken bayani ba kan lamarin, duk da cewa yankin na cigaba da fuskantar hare-hare daga ISWAP da Boko Haram a ‘yan watannin baya.
Baya ga yankin Arewa maso Gabas, sauran sassan Najeriya ma na fuskantar tashin hankali, inda rahotanni suka nuna Amurka ma ta kai farmaki kan ‘yan bindiga a Arewa maso Yamma a baya-bayan nan.














