Afirka

Dakarun Tsaron Nijar Sun Kashe ‘Yan Ta’adda da Kama Mutum 22 Cikin Mako Ɗaya

Dakarun tsaron Nijar sun kashe ‘yan ta’adda da dama tare da kama mutane 22 da ake zargi da laifuka, yayin da suka ƙwace dabbobi, makamai da kuma man gas a samame daban-daban cikin mako guda.

Newstimehub

Newstimehub

11 Mar, 2026

2e7af1d6cc2d25e791392cf2268c93420da2a52c9d6bc5c5546ea57b6f4eff2a

Dakarun tsaron Nijar (FDS) sun kashe wasu ‘yan ta’adda tare da kama mutane 22 da ake zargi da haɗa baki da aikata laifuka a wasu samame da suka gudanar cikin mako guda. Rahotanni sun nuna cewa sojojin sun kai wani hari da bam a kusa da garin Kokorou, inda suka rutsa da ‘yan ta’adda da ke safarar dabbobin da suka kwace daga hannun jama’a.

Harin ya yi sanadin mutuwar biyar daga cikin ‘yan ta’addan, sannan bincike kan gawarwakinsu ya sa aka gano makamai da wasu kayayyakin soji. Haka kuma sojojin sun ƙwace shanu 103 da aka sace daga hannun ɓarayin, inda daga baya aka mayar da su ga masu su.

A wani samame daban a ranar 4 ga Maris a garin Torodi, dakarun Operation Niya sun kashe wani mutum da ake zargi da tattara bayanai domin kai hari kan sojoji. Haka kuma an kama wani mai kwarmata bayanai ga ‘yan ta’adda a wani shingen bincike a Samira, bayan an same shi da waya da wasu kayayyaki da ke nuna alaƙarsa da aikata laifuka.

Bugu da ƙari, jami’an tsaro sun lalata kayayyakin ‘yan ta’adda da ake amfani da su wajen jigilar kaya da haɗa bam a yankin Bankata Gourmantché. A wani samame kuma, dakarun Operation Garkouwa sun kama wata motar dakon mai ta masu safarar mai tare da ƙwace litar man gas 46,000.

Majiyar labari: TRT HAUSA