Fiye da mutane 80, galibinsu mata, sun ɓace a ranar Litinin bayan wasu da ake zargin ‘yanbindiga ne suka yi garkuwa da su a hare-hare biyu daban-daban da suka faru a ƙarshen mako a arewacin Nijeriya.
A ranar Asabar, aƙalla manoma 47 ne wasu ’yanbindiga suka yi garkuwa da su yayin da suke girbin gyada a Jihar Neja, yayin da a ranar Lahadi aka sace mata 40 a Jihar Zamfara da ke maƙwabtaka da ita, a cewar rahotannin tsaro guda biyu da AFP ta gani da kuma wata majiyar yankin.
’Yanbindiga na yawan kai hare-hare kan ƙauyuka, inda suke kashe mazauna tare da ƙona gidaje bayan sun wawushe su. ’Yanta’adda a Nijeriya ma suna amfani da garkuwa da mutane a matsayin hanyar samun kuɗi, kuma a wasu lokuta suna haɗa kai da ƙungiyoyin ’yanbindiga, duk da cewa ’yanbindigar sun fi karkata ne ga neman kuɗi fiye da akida, lamarin da a wasu lokutan ke haifar da faɗa tsakanin ƙungiyoyin.
Mafi yawan waɗanda aka sace a hare-haren baya-bayan nan mata ne
Wata majiyar yankin ta ce an sace manoma 47, mafi yawansu mata, daga gonakinsu da ke Rimi, wani ƙauyen manoma a yankin Mariga na Jihar Neja.
Wani rahoton tsaro da aka shirya wa ƙungiyoyin agaji, wanda AFP ta gani, ya tabbatar da harin, amma bai bayyana adadin mutanen da aka sace ba.
Matan da aka sace a ranar Lahadi kuwa an ɗauke su ne daga Yargada, a yankin Gusau na Jihar Zamfara, a cewar wani rahoton tsaro da aka shirya wa Majalisar Ɗinkin Duniya, wanda AFP ta gani.
Binciken da SBM Intelligence, wata cibiyar tuntuba da ke Legas ta gudanar, ya nuna cewa ƙungiyoyin masu ɗauke da makamai sun karɓi kusan naira biliyan 7.8, wato kusan dala miliyan 6, a matsayin kuɗin fansa tsakanin Yulin 2025 da Yunin 2026. Wannan adadin ya ninka fiye da sau uku na naira biliyan 2.6 da aka biya a matsayin kuɗin fansa a daidai wannan lokaci na shekarar da ta gabata.

















