Wasanni

An yanke wa Tiger Woods hukuncin haramcin tukin mota tsawon shekaru 5 saboda tuki cikin maye

Tiger Woods ya lashe manyan kofunan wasan golf har 15, amma ranar 31 ga Maris ya sanar da cewa zai janye daga wasan golf na “tsawon lokaci don neman magani da mayar da hankali kan lafiyarsa.”

Newstimehub

Newstimehub

2 Sep, 2026

7ac235b4 bb0e 4d7a 9d5d d11cf5d3f1fd 1788355679278

Wata kotu a Florida ta Amurka ta soke lasisin tuƙin mota na shahararren ɗanwasan golf, Tiger Woods, wanda zai hana shi tuƙi tsawon shekaru biyar.

Ranar Laraba ne ɗanwasan ya amsa wasu daga cikin laifukan da ‘yansanda suka tuhume shi, bayan yarjejeniyar amsa laifi don sassaucin hukunci a kotu.

Kotun Martin County Circuit da ke jihar Florida ta kuma ɗora masa tarar dala $1,500, bayan an tuhume shi da laifin tuƙin ganganci da ƙin amincewa da a yi masa gwajin maye bisa doka.

Mai shekaru 50 a duniya, Tiger Woods ya iso kotu ne tare da budurwarsa, Vanessa Trump da kuma lauyansa, Doug Duncan.

Tun ranar 27 ga Maris ne aka kama Woods kan zargin tuƙi cikin maye da kuma ƙin amincewa da umarnin doka, bayan motarsa ta gogi wata tirela da ake ja, har ta kai motar tasa ta gangara a tuntsure.

Da fari, Woods ya ƙi amincewa ya amsa zarge-zargen da aka masa, inda ya shaida wa hukumomi cewa kansa yana ƙasa yana kallon wayarsa kuma yana canja tashar rediyo, wanda ya sa bai ga motar gabansa ta rage gudu ba.

Sai dai jami’an ‘yansandan da suka isa wajen hatsarin sun ce sun tarar da shi yana “gumi kashirɓan” kuma yana motsawa “ba karsashi kuma salo-salo” sanda ake masa intabiyu.

Sai dai gwajin numfashin bakinsa bai nuna akwai barasa a jinisa ba. Amma kuma ya ƙi amincewa a masa gwajin fitsari ko na jini don fayyace ko ya sha ƙwayoyi.

Rayuwar wasa

‘Yansandan sun ce sun gano ƙwayoyi biyu na hydrocodone a aljihun wandonsa, kuma masu gabatar da ƙara sun samu bayani kan ƙwayoyin da likitoci suka rubuta masa.

A rayuwarsa ta wasa, Tiger Woods ya lashe kofunan wasan golf har 15, amma ranar 31 ga Maris ya sanar da cewa zai janye daga wasan golf na “tsawon lokaci don neman magani da mayar da hankali kan lafiyarsa.”

Kuma ya kashe makonni da dama a wata cibiyar marasa lafiya a Switzerland.

Ko a 2017, an taɓa kama Woods kan zargin tuƙi cikin maye, bayan ‘yansanda sun same shi yana barci yayin da yake tuƙi a mota, wadda take da fasassun taya biyu kuma bambar gaba da ta baya a a lalace.

A lokacin Woods ya ce ya sha nau’o’in maganin kashe ciwo. Daga bisani ya amsa laifin tuƙin ganganci sanda ya amince ya shiga shirin maganin a cibiyar magance jarabar shan ƙwaya matsala a shekarar.

A Fabrairun 2021, Woods ya samu munanan raunuka a ƙafa a hatsarin mota guda a wajen Los Angeles, inda motarsa ƙirar SUV mirgina sau da yawa sannan Woods ya maƙale a ciki.

Haka na, an yi masa tiyata a ƙafarsa ta dama, inda har aka saka masa rodi a kashin ƙafa, kuma ya yi zaman asibiti na watanni uku.

Sakamakon, gasar da Tiger Woods ya shiga babbar gasar PGA ta ƙarshe tun a Yulin 2024. A yanzu an shirya zai karɓi baƙi a gasar Hero World Challenge a ƙasar Bahamas a ranakun 3-6 na Disamba.