Shugabannin Faransa, Birtaniya da Jamus sun fitar da sanarwa ta bai ɗaya suna nuna matuƙar damuwa kan rahotannin tashin hankali da jami’an tsaro ke yi wa masu zanga-zanga a Iran.
A cikin sanarwar, Emmanuel Macron, Keir Starmer da Friedrich Merz sun yi Allah-wadai da abin da suka kira kisan masu zanga-zanga, tare da jaddada cewa wajibi ne hukumomin Iran su kare al’ummarsu da kuma ba su ’yancin faɗar albarkacin baki da yin zanga-zanga cikin lumana.
Sun kuma yi kira ga Tehran da ta kauce wa amfani da ƙarfi tare da mutunta haƙƙin ɗan Adam, musamman a wannan lokaci da Iran ke fuskantar zanga-zangar da ta samo asali daga matsanancin matsalar tattalin arziki da faduwar darajar kuɗin ƙasar.
Rahotanni daga ƙungiyoyin kare haƙƙin ɗan Adam sun nuna cewa mutane da dama sun mutu tun bayan ɓarkewar zanga-zangar, yayin da gwamnatin Iran ke zargin ƙasashen waje da tayar da rikicin.














