Ministan Harkokin Wajen Turkiyya, Hakan Fidan, ya gana da Shugaban Rasha, Vladimir Putin, a babban birnin kasar, Moscow, kamar yadda majiyoyin diflomasiyyar Turkiyya suka bayyana.
Ganawar ta fara ne da karfe 7:30 na yamma agogon Moscow, (4:30 na yamma GMT) a ranar Litinin, kuma ta ɗauki kimanin awa guda, in ji majiyoyin.
Sun ce ganawar ta mayar da hankali kan sabbin matakan da ake ɗauka don kawo ƙarshen yaƙin da ake yi tsakanin Ukraine da Rasha, tare da duba ci-gaban da aka samu bayan tattaunawar zaman lafiya da aka gudanar a Istanbul a ranar 16 ga watan Mayu.
Putin da Fidan sun kuma tattauna kan batutuwan da suka shafi dangantakar ƙasashen biyu a fannin tattalin arziki da makamashi.
Tun da farko, Fidan ya gana da Vladimir Medinsky, babban mai shiga tsakani na Rasha a tattauwar Moscow da Kiev.