Yayin da duniya ke ƙara sa ido kan matakan kawo ƙarshen rikicin Gaza, Turkiyya ta tabbatar da rawarta a ƙoƙarin samar da zaman lafiya, inda Ministan Harkokin Wajen ƙasar, Hakan Fidan, zai wakilci Shugaba Recep Tayyip Erdogan a wani muhimmin biki na ƙasa da ƙasa da za a yi a Switzerland.
Ma’aikatar Harkokin Wajen Turkiyya ta sanar da cewa Hakan Fidan zai halarci bikin sanya hannu kan kundin Kwamitin Zaman Lafiya na Gaza, wanda ya zo daidai da fara mataki na biyu na yarjejeniyar tsagaita wuta domin kawo ƙarshen yaƙin Isra’ila a Gaza.
Kwamitin, wanda ake sa ran Shugaba Donald Trump zai jagoranta, zai haɗa da shugabanni daga ƙasashe da dama ciki har da Turkiyya, Birtaniya, Jamus, Faransa, Italiya, Saudiyya, Qatar da Masar, tare da sa ido kan kafa gwamnatin ƙwararrun Falasɗinawa da kuma sake gina Gaza. Wannan shiri wani ɓangare ne na kudurin MDD mai lamba 2803 da ya amince da shirin zaman lafiya na matakai 20 da Trump ya gabatar.














