Gwamnatin tarayya ta Somalia ta sanar a daren Lahadi cewa wa’adin shugabancin jihar South-West da kuma gwamnatinta ya kare, a daidai lokacin da rikici ke kara tsananta tsakanin bangarorin biyu. Ma’aikatar harkokin cikin gida ta bayyana cewa ba za ta sake amincewa da duk wani nadin mukami ko sauyi da gwamnatin jihar ke yi ba.
Sai dai gwamnatin ta ce hukumomin kananan hukumomi za su ci gaba da gudanar da ayyukansu har sai an zabi sabbin majalisu. Haka kuma ta ce tana tuntubar dattawan gargajiya domin tabbatar da zaman lafiya da hana rikici. Ma’aikatar ta jaddada cewa ita ce za ta jagoranci wannan tsari tare da hadin gwiwar shugabannin gargajiya.
Rikicin siyasar ya kara tsananta ne bayan majalisar dokokin kasar ta amince da sauya kundin tsarin mulki, lamarin da ya kawo karshen tsarin rikon kwarya da aka shafe shekaru ana yi. Jihar South-West ta yi watsi da gyaran, tana mai zargin cewa cike yake da magudi da kuma cin hanci.
Bangaren gwamnatin tarayya na zargin shugaban jihar, Abdiaziz Laftagareen, da mulki ba bisa ka’ida ba, yayin da jami’an jihar ke kallon matakin gwamnatin tarayya a matsayin tsoma baki da yunkurin kakaba shugaba. Bayan dakatar da hadin kai, jihar ta kuma zargi gwamnatin da goyon bayan wasu ‘yan bindiga domin tayar da zaune tsaye.
Bugu da kari, jihar ta dakatar da dukkan zirga-zirgar jiragen sama na kasuwanci da masu zaman kansu, tana mai cewa matakin na tsaro ne. An ce jiragen Majalisar Dinkin Duniya da Tarayyar Afirka kadai za su ci gaba da aiki, kuma an takaita su ga ayyukan jin kai, lafiya da na hukuma.














