Kasuwanci Tsaro

Harin Burkina Faso ya haddasa tashin farashin tumatur a Ghana

Tsaikon jigilar tumatur daga Burkina Faso ya haddasa tashin farashi a kasuwannin Ghana.

Newstimehub

Newstimehub

25 Feb, 2026

2025 12 13t050835z 346853039 rc2xaia6j85l rtrmadp 3 travel cm accra

Wani hari da ’yan ta’adda suka kai a Burkina Faso ya fara yin tasiri kan farashin tumatur a wasu yankunan Ghana. Rahotanni daga kasuwannin Denu da Agbozume a Ketu South sun nuna cewa farashin ya yi tashin gwauron zabi, lamarin da ya jefa masu saye da ’yan kasuwa cikin damuwa.

Tumatur da Ghana ke samu galibi daga Burkina Faso ya yi tsada bayan harin ya kawo tsaiko ga hanyoyin fatauci da jigila. Binciken farashin kasuwa ya nuna cewa kwandon tumatur da a baya ake sayarwa GHS30 ya tashi zuwa GHS50, yayin da ƙaramin kwando ya koma GHS30 zuwa GHS35 daga GHS20.

Masu sayar da tumatur sun danganta hauhawar farashin da ƙarancin kaya da kuma matsalolin sufuri. Wasu sun ce shigar tumatur daga Burkina Faso ya ragu sosai tun bayan harin, abin da ya kara tsananta tsadar.

Majiyar Labari: TRT HAUSA