Wani mummunan hatsarin jirgin sama mai saukar ungulu ya girgiza al’ummar Kenya a ranar Asabar bayan ya yi ajalin mutane shida, ciki har da dan majalisa mai wakiltar mazabar Emurua Dikirr. Lamarin ya faru ne a gundumar Nandi da ke yankin North Rift, inda jami’an tsaro suka tabbatar da faruwar hatsarin.
Kwamandan ‘yan sandan yankin, Samuel Mukusi, ya shaida wa gidan talabijin na Citizen TV cewa dan majalisar, matukin jirgin da wasu mutum huɗu sun rasu a wurin. Har yanzu ba a bayyana musabbabin faduwar jirgin ba, yayin da ake ci gaba da bincike domin gano abin da ya haddasa hatsarin.
Shugaban ƙasar Kenya, William Ruto, ya bayyana sunan dan majalisar a matsayin Johana Ng’eno, mai shekaru 53, wanda ya fara zama dan majalisa tun 2013 sannan aka sake zaɓensa a 2017 da 2022. Shugaban ya miƙa sakon ta’aziyya ga iyalai da abokan arzikin mamacin tare da al’ummar mazabarsa.
Har zuwa lokacin fitar da wannan rahoto, ba a bayyana sunayen sauran mutanen da hatsarin ya rutsa da su ba.














