Nijeriya

Hedikwatar tsaron Nijeriya ta tattauna da jakadan Saudiyya kan ƙarfafa alaƙar tsaro

Wata sanarwa daga hedikwatar tsaron ta ambato jakadan yana bayyana sha’awarsa ta ƙarfafa dangantaka tsakanin Saudiyya da Nijeriya, wadda ya bayyana a matsayin muhimmiyar abokiyar aiki a Afirka.

Newstimehub

Newstimehub

27 Aug, 2026

d8387bf9 d4b3 40ef 9f83 ce3eafcb1c6c 1787827245758

Hediwakatar Tsaron Nijeriya ta ce ta tattauna da Jakadan Saudiyya a Nijeriya, Yousef bin Mohammed Al-Balawi, kan ƙoƙarin ƙarfafa alaƙar soji tsakaninsu yayin da suke neman ƙarin fannonin taimaka wa juna.

Hedikwatar ta bayyana wannan ne a wata sanarwar da fitar game da ziyarar da Jakadan Saudiyya a Nijeriya, Yousef bin Mohammed Al-Balawi ya kai Hedikwatar Tsaron Nijeriya, da zummar ƙarfafa dangataka tsakanin ƙasashen biyu da kuma danganataka ta tsaro.

A wata sanarwar da ta fitar a ranar Laraba Darakatan Watsa Labaran Hedikwatar Tsaron, Manjo Janar Samaila Uba, ya ambato Babban Hafsan Tsaron Nijeriya, Janar Olufemi Oluyede yana bayyana muhimmancin da Nijeriya ta bai wa dangatakarta da Saudiyya yayin da yake karɓar jakadan.

Janar Oluyede ya ce akwai buƙatar ci gaba da kuma faɗaɗa hanyoyin haɗin kai da tsakanin ƙasashen biyu, musamman a fannonin da za su inganta ƙwarewar aiki da kuma ingnacin aikin sojin Nijeriya, in ji sanarwar.

Kazalika sanarwar ta ambato jakadan yana bayyana sha’awarsa ta ƙarfafa dangantaka tsakanin Saudiyya da Nijeriya, wadda ya bayyana a matsayin muhimmiyar abokiyar aiki a Afirka.

Jakadan ya ce a shirye Saudiyya ta ke wajen ƙarin haɗin kai tsakanin ƙasashen biyu musamman a fannin tsaro.

“Ɓangarorin biyu sun amince cewa dangataka ta hukumomi da aiki tsakanin dakarun sojin ƙasashen biyu za su ba da gudumuwa wajen inganta haɗin kai wajen magance matsalolin tsaron da ƙasashen biyu ke fama da su,” in ji sanarwar.

Sanarwar ta ƙara da cewa babban hafsan tsaron Nijeriya ya bayyana jin daɗinsa ga jakadan kan yadda Saudiyya ke ci gaba da fatan alkhairi ga Nijeriya yana mai fatan cewa tattaunawar za ta samar da hanyoyin haɗin kai a aikace.