Kafofin yada labarai na gwamnati a Iran sun ruwaito cewa hukumomin tsaron teku sun ƙwace wani jirgin dakon mai a kusa da tsibirin Qeshm da ke kudancin ƙasar, bayan gano cewa yana ɗauke da lita miliyan huɗu na fetur da aka yi fasa-ƙwauri.
Hukumomi sun ce an tsare ma’aikatan jirgin su 16, dukkansu ’yan ƙasashen waje, bisa zargin hannu a safarar man fetur ba bisa ƙa’ida ba. Sai dai ba a bayyana sunan jirgin ko ƙasar da ya fito ba.
Gidan talabijin na gwamnati ya bayyana cewa an kama jirgin ne a ranar Laraba, yayin da shafukan labarai na intanet suka wallafa bidiyo da hotuna na abin da suka ce shi ne jirgin da aka ƙwace.
Wannan ba shi ne karo na farko ba. A makon da ya gabata, Iran ta ce ta ƙwace wata tankar mai a Tekun Oman da ke ɗauke da lita miliyan shida na dizal da aka shigo da shi ba bisa ƙa’ida ba, duk da cewa har yanzu ba a bayyana bayanan jirgin ba.
Masana na cewa Iran na fuskantar matsalar yawaitar safarar mai saboda rangwamen farashin fetur a ƙasar, wanda ke faruwa sakamakon tallafin gwamnati da kuma faɗuwar darajar kudin Iran. Hakan ya sa ake safarar man ta ƙasa zuwa ƙasashen makwabta da kuma ta teku zuwa ƙasashen yankin Gulf.














