Nijeriya

Kotu ta yanke wa mutumin da ya kashe matarsa hukuncin kisa a jihar Yobe ta Nijeriya

Kazalika alƙalin ya ce masu gabatar da ƙarar sun tabbatar da tuhumar aikata lafin zuwa wani mataki da ya zarce shakka.

Newstimehub

Newstimehub

22 Oct, 2026

b425959d 1540 47e0 84a3 d201263f9179 1792657761951

Wata babbar kotun jihar Yobe a arewa maso gabashin Nijeriya ta yi wa wani mutum mai suna Abubakar Musa hukuncin kisa ta hanyar rataya bayan ta same shi da laifin kashe matarsa.

Gidan talbijin na Nijeriya, NTA, ya ruwaito cewa kotun mai zama a Damaturu, babban birnin jijhar ta Yobe ta samu Abubar Musa mai shekara 45, wanda ake yi wa laƙabi da Daddy da laifin kashe matarsa mai suna Ammi Mamman ne a shekarar 2024.

A ranar 4 ga watan Janairun shekarar 2024 ne dai rundunar ‘yansandan jihar Yobe ta kama mutumin bayan an zarge shi da kashe Ammi a rukunin gidajen New Bra-Bra Housing Estate da ke Damaturu kuma ta gurfanar da shi a gaban kotu.

Bayan shekara biyu, alƙalin babban kotun jihar Yobe na 1 ya yi watsi da iƙirarin Daddy na cewa ba shi da laifi, yana mai cewa bisa dalilan da suke gabansa irin wannan iƙirarin ba zai karɓu ba kuma masu gabatar da ƙara sun tabbatar da dukkan bayanai na laifin kisan kai.

Kazalika alƙalin ya ce masu gabatar da ƙarar sun tabbatar da tuhumar aikata laifin zuwa wani mataki da ya zarce shakka.

A bisa doka, Daddy na da ‘yancin ɗaukaka ƙara cikin ranakun da aka yarda ya ɗaukaka ƙarar ko kuma a aiwatar da hukuncin idan bai ɗaukaka ƙarar ba, in ji rahoton na NTA.