Wata Kotun Tarayyar Nijeriya a babban birnin ƙasar Abuja ta yi wa tsohon muƙaddashin babban akantan ƙasar ɗaurin shekara 72 kan laifin halasta kuɗin haram.
Da yake yanke hukuncin ranar Litinin alƙalin kotun, James Omotosho, ya yanke hukuncin cewa hukumar yaƙi da masu yi tattalin azikin Nijeriya zagon ƙasa (EFCC) ta tabbatar da tuhume-tuhumenta kan tsohon muƙaddashin akantan Anamekwe Nwabuoku.
An gurfanar da Nwabuoku a gaban kotun ne kan tuhume-tuhume da suka haɗa da halasta kudin haram da damfara kan kuɗin da ya kai naira miliyan N868.4 .
An ba da belinsa kan kuɗi naira miliyan N500 da masu tsayawa biyu da ke da kimar irin kudin.
An samu Nwabuoku da laifin aikata tuhume-tuhumen guda tara kuma aka yi masa ɗaurin shekara takwas kan ko wace tuhuma, lamarin da ya mayar da ɗaurinsa na shekara 72.
Sai dai kuma kotun ta ba da umarnin cewa ɗaurin na shekara takwas takwas za su aiki ne a lokaci ɗaya.
Omotosho ya bayyana yadda Nwabuoku ya juya akalan kuɗaɗen da aka ware domin tsaro a lokacin da yake aiki a matsayin darakatan kudi da asusun kuɗaɗe a ma’akatar tsaro a matsayin “ abin taƙaici.“
Alƙalin ya kuma yaba wa hukumar EFCC kan abin da ya bayyana a matsayin aiki tuƙuru wajen gurfanar da lamarin a gaban kotu.
Ya bayyana cewa lauyoyin wanda ake tuhuma ba su musanta shaidar mutum na tara da masu gabatar da ƙara suka gabatar a matsayin shaidu— cewa Nwabuoku ya dawo da naira miliyan N200 da kansa a lokacin bincike.
Tsohon shugaban Nijeriya, Muhammadu Buhari ne ya naɗa Nwabuoku a matsayin muƙaddashin akanta janar na Nijeriya ranar 20 ga watan Mayu ta shekarar 2022 bayan an dakatar da Ahmed Idris kan tuhumar damfarar naira biliyan N80 .
Sai dai kuma cikin ‘yan makonni aka cire Nwabuoku daga muƙamin a cikin watan Juli bayan rahotannin sun fito suna bayyana cewa hukumar EFCC tana bincike a kansa.














