Gwamnatin Tarayyar Nijeriya ta karyata rahotannin da ke cewa ta biya makudan kudaden fansa tare da sakin wasu kwamandojin ’yan bindiga domin kubutar da daliban makarantar St. Mary’s da ke Jihar Neja. A wata sanarwa da Ministan Yaɗa Labarai, Mohammed Idris, ya fitar, gwamnatin ta bayyana zarge-zargen a matsayin ƙarya marar tushe.
Sanarwar ta jaddada cewa babu wani kudin fansa da aka biya, kuma ba a saki wani kwamandan ’yan bindiga ba. Gwamnatin ta ce irin wadannan rahotanni na tauye ƙwarewa da sadaukarwar jami’an tsaro, tana mai zargin cewa an dogara ne kan majiyoyi marasa suna maimakon bayanan hukuma.
Hukumomin tsaro da suka hada da ONSA da DSS, tare da shugabannin Majalisar Dokoki, sun fito fili sun musanta batun. An kuma karyata zargin cewa an kai kudin fansa ta jirgin sama mai saukar ungulu, inda DSS ta kira batun kirkirarren labari.
Gwamnatin Tarayya ta ce an samu nasarar kubutar da daliban ne ta hanyar leƙen asiri da tsare-tsaren aiki na musamman ba tare da rasa rai ba. Ta kuma bukaci kafafen yada labarai da su rika tantance bayanai kafin wallafawa, domin kauce wa yada rahotannin da ka iya rage ƙwarin gwiwar jami’an tsaro.














