Rikicin siyasa da shari’a ya ƙara ɗaukar sabon salo a Venezuela, yayin da tsohon shugaban ƙasar, Nicolas Maduro, ke shirin bayyana gaban kotu a Amurka, a daidai lokacin da wasu ƙasashe ke nuna damuwa kan tsoma bakin waje a harkokin ƙasar.
Tsohon shugaban Venezuela, Nicolas Maduro, ana sa ran zai bayyana gaban wani alƙalin tarayya a birnin New York da tsakar rana ranar Litinin, domin sanar da shi a hukumance tuhume-tuhumen da ake yi masa. Kotun ta ce za a gabatar da shi ne bayan da sojojin Amurka suka cafke shi tare da matarsa, Cilia Flores, a wani samame da aka kai Caracas da asubahin Asabar.
Ana zargin Maduro da laifin “narcoterrorism”, wato hannu a safarar miyagun ƙwayoyi, musamman hodar iblis, zuwa cikin Amurka. An kwashe shi zuwa New York domin fuskantar shari’a bisa zargin da ya shafi safarar tan-tan na kwayoyi.
A gefe guda kuma, ƙasashen Brazil, Chile, Colombia, Mexico, Uruguay da Spain sun fitar da sanarwa tare, inda suka yi Allah-wadai da duk wani yunƙurin waje na karɓar iko ko sarrafa albarkatun Venezuela. Wannan martani ya biyo bayan kalaman Shugaban Amurka Donald Trump, wanda ya ce Washington na iya “tafiyar da” Venezuela tare da samun damar man fetur ɗinta.
Ƙasashen sun bayyana rashin amincewarsu da kifar da Maduro ta hanyar amfani da ƙarfi, tare da nuna damuwa kan duk wani yunƙuri na mamaye iko ko albarkatun ƙasa da ke da muhimmanci ga Venezuela. A halin yanzu, Trump ya yi barazanar cewa shugabar rikon kwarya ta ƙasar, Delcy Rodriguez, za ta fuskanci mummunan sakamako idan ba ta yi aiki da muradun Amurka ba.
Rodriguez dai ta samu amincewar Kotun Ƙoli da rundunar sojin Venezuela a matsayin shugabar rikon ƙwarya. Duk da cewa Trump ya sha suka kan sauya gwamnatoci a ƙasashen waje, ya bayyana cewa Amurka za ta iya “sake gina” Venezuela, yana mai cewa ƙasar ta faɗa cikin mummunan hali na durƙushewa.














