Kwamitin Kasafin Kuɗi na Majalisar Dokokin Amurka zai gudanar da wani muhimmin taro a ranar Talata domin tattaunawa kan ƙara ta’azzarar rashin tsaro da kuma zargin cin zarafin ‘yancin addini a Nijeriya, musamman kan Kiristoci.
Sanarwar da ɗan majalisar Riley Moore ya wallafa ta tabbatar da cewa Mario Díaz-Balart — mataimakin shugaban kwamitin kasafin kuɗi kuma shugaban kwamitin tsaro — zai jagoranci zaman tare da wakilan kwamitin harkokin waje da sauran kwararru.
A taron za a saurari rahotanni daga kwamitin Amurka kan ‘yancin addini na duniya, tare da tattara shaidu game da tashin hankali da laifukan da ake zargin ana aikatawa kan Kiristoci a Nijeriya.
Taron dai na zuwa ne a daidai lokacin da Amurka da Nijeriya ke ƙara zurfafa haɗin gwiwar yaki da ta’addanci, bayan ziyarar da tawagar tsaro ta Nijeriya ta kai Washington a baya-bayan nan.
Gwamnatin Nijeriya ta jaddada cewa tana ɗaukar matakai don kare ‘yancin addini da samar da tsaro ga al’ummarta, duk da cewa rahotanni da shaidu daban-daban na ci gaba da jawo hankalin duniya kan lamarin.














